1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mosko na adawa da tsagaita wuta a Aleppo

Mohammad Nasiru AwalAugust 15, 2016

Sergey Lavrov ya yi watsi da kiran da Farnk-Walter Steinemeier ya yi na tsagaita a Aleppo duk da mawuyacin hali da mazauna birnin ke ciki.

https://p.dw.com/p/1JiXe
Russland Frank-Walter Steinmeier und Sergei Lawrow in Jekaterinburg
Hoto: picture-alliance/dpa/TASS/D. Sorokin

A wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier da ke wata ziyara a Rasha, takwaran aikinsa na Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da kiran da Steinmeier din ya yi na tsagaita wuta a birnin Aleppon kasar Siriya. Shi dai ministan harkokin wajen na Jamus ya bukaci Rasha da ta tsagaita wuta don bada damar kai kayan agaji a Aleppo. A lokacin da yake magana da manema labarai bayan sun gana a yankin Yekarerinburg na Rasha, Lavrov ya yi nuni da yarjeniyoyin da ke kasa. Da kuma ya juya kan halin da ake ciki a Ukraine, Lavrov cewa ya yi:

"Ko shakka babu aiwatar da matakan kawo karshen rikicin Ukraine zai inganta halin da ake ciki. Wannan zai yiwu ne idan muka ci-gaba da martaba tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar birnin Minsk, wanda Rasha da Jamus ke ciki. Wannan shi ne matsayinmu."