1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mubarak zai sake gurfana a kotu?

March 3, 2013

A ranar 13 ga watan Afrilu tsohon shugaban Masar, Husni Mubarak zai sake gurfana a gaban kotu bisa zargen da ake masa na kashe masu zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/17pVv
Hoto: dapd

Kamfanin dillacin labarun kasar ta Masar wato MENA ya ce kotun daukaka kara da ke birnin Alkahira ce ta kebe wannan rana. A wancan shekara ne aka yanke wa tsohon shugaban da ke fama da rashin lafiya hukuncin daurin rai da rai a gidan yari. A dai halin yanzu Mubarak dan shekaru 85 yana kwance a wani asibitin soji inda yake karbar magani. A watan Janairun da ya gabata ne aka mika bukatar sake gurfanar da shi a gaba kuliya. Lauyoyinsa sun bayyanar da wannan hukunci tamkar kuskure. Sun kuma yi korafin cewa an yi musu rashin adalci wajen gudanar da aikisu. Akwai 'yan kasar ta Masar da dama da ke mamakin rashin yanke masa hukunci bisa laifin kashe masu zanga-zanga a watan Janairun shekarar 2011.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu