1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugun Baƙo–Sauro

January 18, 2010
https://p.dw.com/p/LYsp
Hoto: LAI F


'Yan ƙananan ƙwari ne dake kai hari a cikin dare kuma su kan kai mutum su baro: wato sauro dake yaɗa zazzaɓi. Zazzaɓin cizon sauro na ɗaya daga cikin cututtukan da suka fi halaka mutane a Afirka. Amma fa riga kafinsa ba shi da wahala.


Zazzaɓin cizon sauro na ɗaya daga cikin manyan annobar Afirka. Ya kan kashe mutane kusan miliyan ɗaya a shekara a faɗin duniya. Kashi 90 cikin ɗari na masu mutuwar a Afirka suke. Matsalar ta fi shafar mata masu juna biyu da yara ƙanana. Galibi matalauta su ne suka fi fama da raɗaɗi saboda sau tari ba su da ikon neman magani da zarar sun fara ganin alamun cutar a jikinsu.

A haƙiƙa dai riga kafi ya fi magani. Akwai wasu nau'o'i na zazzaɓin cizon sauro da ba a iya warkar da su da magungunan da aka saba amfani da su ba. Amma riga kafi shi ne mafi sauƙi. Misali amfani da gidan sauro ko kuma sanya riguna masu dogayen hannu da zarar almuru ya shiga.

Domin jin ƙarin bayani mai amfani sai a saurari sabuwar salsalar shirinmu akan zazzaɓin cizon sauro. Zamu kasance ne tare da wasu 'yan Afirka dake ƙoƙarin shawo kan zazzaɓin cizon sauro. A kan hanya zasu koya mana irin abubuwan da zamu iya yi don tinkarar cutar.