1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan amincewa da Palestinu a Majalisar Dinkin Duniya

November 29, 2012

Palestinu ta samu goyan bayan ƙasashe da dama a ƙoƙarin samun matsayin kujera 'yar kallo a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/16smj
Mahmoud Abbas, Chairman of the Executive Committee of the Palestinian Liberation Organization and President of the Palestinian Authority, addresses to the 67th United Nations General Assembly meeting September 27, 2012 at the United Nations in New York. AFP PHOTO / DON EMMERT (Photo credit should read DON EMMERT/AFP/GettyImages)
Mahmoud AbbasHoto: AFP/Getty Images

Tun a shekara 1947 Majalisar Dinkin Duniya ta rattaba hannu kan ƙudurin girka ƙasar Isra'ila,da kuma Palestinu a matsayin ƙasashe biyu masu maƙwaftaka da juna, to amma yau shekarau 65 kenan da suka gabata ake ta kai ruwa rana game da batun girka ƙasar Palestinu da samar mata kujera a Majalisar Dinkin Duniya ba tare da an cimma nasara ba.

To amma a 'yan shekarun baya-bayan nan, palestinawa sun fara sa kwaɗayin samun ƙasa mai zaune da gindin kanta.A shekara da ta gabata duk da tsananin adawar Amurika da Isra'ila, Palestinu ta yi nasara zama memba a hukumar al'adu da kimiya ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO, sai kuma a yau inda, ga dukan alamu haƙar Mahmud Abbas shugaban hukumar Palestinawa za ta cimma ruwa, domin ko kamin kaɗa ƙuri'a ƙasashe, da dama sun baiyana aniyarsu ta amincewa da baiwa Palestinu kujera 'yar kallo a zauren Majalisar Dinkin Duniya, matakin da a cewar Yossi Mekelberg masani a cibiyar kimiyar siyasa ta Chatham da ke birnin London ya yi daidai:

"Wannan mataki na matsayin gagaramar galaba ga Palestinu, sannan kuma a diplomasiyance, koma baya ne ga Isra'ila,wadda ta ke masa kallon barazana ga al'amuran tsaronta".

Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu gestures as he delivers a statement to the press at his Jerusalem office on November 21, 2012. Israel and Hamas agreed on a truce that will take effect this evening in a bid to end a week of bloodshed in and around Gaza that has killed more than 150 people, Egypt and the United States said. AFP PHOTO/GALI TIBBON (Photo credit should read GALI TIBBON/AFP/Getty Images)
Benjamin NetanyahuHoto: GALI TIBBON/AFP/Getty Images

Shi kuwa Xavier Abu Eid, ɗaya daga membobin komitin da ke kula da samar wa Palestinu kujera a Majalisar Dinkin Duniya cewa yayi burinsu shins na samar da ƙasashe biyu wato Isra'ila da Palestinu wanda za su zama cikin yanayi irin na cuɗe- ni- in -cuɗe ka, saboda haka, akwai buƙatar samun haɗin kai daga ƙasashen duniya.

"Wajibi ne gamayyar ƙasa da ƙasa ta amincewa Palestinu kaiwa ga wannan matsayi.An jimma ana ta tafaka mahauwarori game da batun,shin minene leffi, dan Palestinu ta zama 'yar kallo kawai a zauren Majalisar Dinkin Duniya".

Ko da ya ke buƙatar Palestinawa itace samun ƙasa mai cikkaken 'yanci,amma sannu-sannu ba ta hana zuwa inji Abu Eid.

Saidai a tunanin hukumomin bani Yahudu, Palestinu ta ɗauki wannan mataki gaba gaɗi ba tare da shawara ba, kamar yadda Paul Hirschson kakakin ministan harkokin wajen Isra'ila ya nunar:

"Wannan aniya ta Palestinu ta saɓawa yarjejeniyar da muka rattaba wa hannu a birnin Oslo, wadda ta tanadi warware rikicin ta hanyar shawarwari tsakanin Isra'ila da Palestinu".

President Barack Obama shakes hands with Palestinian President Mahmoud Abbas and Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu after delivering remarkes on the Middle East peace negotiations in the East Room of the White House in Washington, Wednesday, Sept. 1, 2010. (AP Photo/Charles Dharapak)
Obama, Netanyahu da AbbasHoto: AP

A Isra'ila ta sha alwashin ɗaukar hanyoyin ƙafar angulu ga yunƙurin na Palestinu, wanda a cewarta ba zai taimaka ba, wajen cimma masalaha.

Shima Yossi Mekelberg duk da haɗin kai da ya bayar game da karɓar Palestinu a Majalisar Dinkin Duniya, ya na daga masu tunanin cewa cigaban da aka samu irin na mai haƙar rijiya ne, muddun Isra'ila ba ta daina gine-gine a yankunan Palestinawa ba.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Halima Balaraba Abbas