1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawarar kungiyar AU kan ficewa daga ICC

October 11, 2013

Kasashen Afirka da ke zaman mambobi a kungiyar nan ta AU sun hallara a kasar Habasha domin tattaunawa da kuma yin muhawara kan ficewa daga jerin mambobin kotun ICC.

https://p.dw.com/p/19xqA
Newly elected South African minister Nkosazana Dlamini-Zuma as first female head of the African Union (AU) Commission, speaks during a press conference on July 16, 2012 during the 19 African Union Summit in Addis Ababa. As head of the organization's executive arm, Dlamini-Zuma faces immediate challenges as the AU tries to gain UN Security Council backing for a military intervention in northern Mali, where local and foreign al-Qaeda-linked jihadists seized control after a destabilising coup in the southern capital Bamako. AFP PHOTO/SIMON MAINA (Photo credit should read SIMON MAINA/AFP/GettyImages)
Hoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

A wannan Juma'ar ce kungiyar kasashen Afirka ta AU ke fara wani taro na kwanaki biyu domin yin muhara kan ficewar wasu kasashen Afirka daga jerin kasashen da suka amince da kotun na da ke hukunta laifukan yaki ta kasa da kasa da ke Hague a kasar Holland.

Kasashen na Afirka dai sun yake yin wannan muhara ce saboda zargin da dama ke yi cewar kotun na yin shari'a ne kawai ga shugabannin Afirka maimakon na kasashen duniya baki daya.

Gabannin wannan muharawa dai, kungiyar ta AU ta bukaci kotun da ta ICC da ta jingine shari'ar da ta ke yi wa shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto bisa zargin hannun da suke da shi wajen tada zaune bayan zaben shugaban kasar na 2007 da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

A watan Satumban da ya gabata dai Kenya ta wuce gaba wajen ficewa daga cikin mambobin kutun bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da haka.

To sai dai a daura da wannan, ministar harkokin wajen Kenya Amina Muhammad tace Kenya ba ta neman kasahen Afirka su juyawa kotun baya, sai dai a yi kokarin ganin kotun ta daidaita al'amuranta.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe