1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mujuru ta Zimbabuwe ta kafa jam'iyyarta

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 1, 2016

Joice Mujuru da ke zama tsohuwar mataimakiyar shugaba Mugabe ta ce ta kafa wannan jam'iyyar domin kawo karshen cin hanci da danniyr a wannan kasa ta Zimbabuwe.

https://p.dw.com/p/1I58Q
Afrika Simbabwe ehemalige Vizepräsidentin Joice Mujuru bei Pressekonferenz
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Shekara guda da rabi bayan tsigeta daga mukaminta, tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Zimbabuwe Joice Mujuru, ta kaddamar da jam'iyyarta mai suna Zimbabwe People First. A lokacin wani taron manaima labarai da ta gudanar da birnin Harare, Mujuru ta ce ta kafa wannan jami'iyya ne don yaki da mulkin danniya da ake gudanarwa a Zimbabuwe tun bayan da ta samu 'yancin kanta a shekarar 1980.

Ita dai Joyce Mujuru ta shafe shekaru 30 a cikin jam'iyyar Zanu-PF da ke mulki kafin shugaba Mugabe ya koreta saboda abin da ya kira zagon kasa da ta ke yi wa mulkinsa.

A lokacin da take mayar da martani a kan cin mutuncin da uwargidan shugaba Mugabe wato Grace ke yi mata, Mujuru ta ce ba abin da ya hadata da kisan kai da kuma maita da ake zarginta da mara.

Tuni dai wasu tsofoffin ministocin gwamnatin Mugabe suka rungumi wannan sabuwar jam'iyya. Sai dai ana ganin cewar Mujuru mai shekaru 60 a duniya za ta fuskanci kalubale wajen samar wa jam'iyarta da tagomashi a Zimbabuwe.