1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Munanan hare-hare sun kashe mutane 46 a Jos

May 20, 2014

Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 46 bayan wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da aka kaddamar a birnin Jos na jihar Plateau na Najeriya.

https://p.dw.com/p/1C3T9
Hoto: dapd

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kaddamar a birnin Jos na jihar Plateau na Najeriya sun salwantar da rayukansu mutane 46. Hukumomi da su ka yi bayani game da adadin wadanda hare-haren suka ritsa da su, sun kuma ce mutane 45 sun samu raunuka..

Jami'an agajin gaggawa na NEMA suna kokarin kai gawarwaki zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Jos. Kana wadanda suka samu raunuka na karban magani a asibitoci mafi kusa.Da misalin karfe uku na rana ne wani abu da ake zaton bam ne ya fashe a kasuwar Terminus. Yayin da na biyun kuma ya tashi duk a yanki guda jim kadan bayan na farkon.

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin wadannan hare-hare ya zuwa yanzu. Sai dai kuma kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ta daukin alhakin hare-haren da suka wakana a wani coci a shekara ta 2011. Sannan kuma wannan birnin na Jos dai ya zama fuskantar rikici na kabilanci da kuma na addini.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu