1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muradun Nijer a kokarin warware rikicin Mali

March 5, 2013

Nijer ta ce tarayyar da arewacin kasar ke yi da Mali ta fuskar al'adu da zamantakewa ne ya tilasta mata tsoma baki a rikicin Mali.

https://p.dw.com/p/17qci
Hoto: Eric Feferberg/AFP/Getty Images

Juyin mulkin watan Maris daya afku a Mali da kuma mamaye yankin arewacin kasar da 'yan tawaye tare da hadin gwiwar masu tsananin kishin addini suka yi, shi ne tunda farko ya fara jefa damuwa a Nijer, kasancewar tana da tarihin fuskantar irin wadannan matsaloli, domin kuwa jamhuriyyar Nijer na da dadadden tarihin 'ya tawaye, wanda ma kimanin shekaru ukkun da suka gabata ne ta yi nasarar cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe tare da su, ga shi kuma a cikin watan Afrilun shekara ta 2011 ne zaben shugaba Mouhamdou Issoufou na Nijer ya kawo karshen mulkin soji a kasar.

A bisa wannan dalili ne gwamnatin Nijer ta bayyana takaicinta game da tsawon lokacin da mahukunta a birnin Bamako, fadar gwamnatin Mali suka dauka na yin watsi da harkokin tsaro a yankin arewacin Mali, inda suka kyale bata-gari na safarar muggan kwayoyi da kuma makamai ba tare da shawo kan matsalar tun kafin ta yi karfi ba.

Ministan kula da harkokin wajen jamhuriyyar Nijer Bazoum Mohamed, ya ce matsalar ta zama babbar barazana ga jamhuriyyar Nijer musamman bayan kawar da gwamnatin shugaba Mouamer Gaddhafi na Libiya :

Ya ce " Ba mu da karfin azo a gani sabanin abokan gabanmu. Saboda haka ne muka yi kira ga kawayenmu wadanda muka hada guywa da su domin dakile rikicin na arewacin Mali. Wannan ne zai bai wa 'yan Nijar damar barci ba tare da fargaba ba."

Muhimmiyar gudummowar da Nijer ta bayar dai ita ce tura dakarunta zuwa Mali da ke makwabtaka da ita. Bugu da kari, ta samar da sansani ga jiragen yakin Amirka - masu sarrafa kansu da kansu a wajen babban birnin kasar. Sai kuma wasu dakarun sojin da Faransa ta tura zuwa yankin arewacin na NIjer domin bayar da tsaro ga wuraren hako ma'adinai na kasar da kanfanin Areva na Faransa ke yi.

Titel: Seini Oumarou, Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Schlagworte: Niger, Oumarou, Opposition, MNSD Wer hat das Bild gemacht?: offizielles Bild (MNSD) Wann wurde das Bild gemacht?: 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Niamey, Niger Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Seini Oumarou ist Vorsitzender der Partei MNSD-Nassara (Mouvement National de la Société de Développement ) und seit April 2011 Oppositionsführer im Niger. Zuvor hatte er in der Stichwahl um die Präsidentschaft gegen Mahamadou Issoufou verloren.
Shugaban adawa a Nijer, Seini OumarouHoto: MNSD

Matsayin 'yan adawa game da rikicin Mali

'Yan adawa a Nijer dai sun bayyana goyon bayan su ga irin matakan da hukumomin suka dauka, kamar yanda jagorar adawa a kasar Seini Oumarou ya shaidawa tashaw DW cewar yana tuntubar shugaban kasa akai-akai game da batun na Mali:

Ya ce " Gwamnati ta tura da kudirin doka a majalisa domin neman ta bayar da izinin tura sojoji Mali. 'Yan adawa sun yi na'am da wannan kudiri. Mun bayar da shawarwari da suka hada da sanar da 'yan kasa halin da dakaru Nijar ke ciki a Mali daga lokaci zuwa lokaci."

Kungiyoyin farar hula na adawa da jibge sojin ketare a Nijer

Sai dai kuma akwai wadanda ke yin adawa da matakin tura sojojin zuwa Mali, inda Moussa Tchangari, da ke zama dan jarida kana mai fafutukar kare hakkin bil'Adama ya jaddada bukatar kungiyar tattalin arzikin yammacin Afirka ta yi anfani da hanyar sulhu domin samun mafita a rikicin na Mali:

Ya ce " Abinda ma nake ganin ya fi muni shi ne jibge dakarun kasashen ketare a kasarmu Nijer. Ba ma adawa da tura dakaru zuwa Mali, amma kyale dakarun ketare su kafa sansanin su a Nijer yana da hatsari sosai, domin kuwa hakan zai sa wadanda ake yaka za su iya kai mana hari."

Moussa Tchangari ist Journalist und Menschenrechtler im Niger. Er ist Generalsekretär der Organisation "Alternative Espaces Citoyens" 25.2.2013
Moussa Tchangari,Hoto: DW/ Thomas Mösch

Gujewa hatsarin farmakin ne yasa - jim kadan bayan barkewar rikicin na Mali, gwamnatin Jamus ta rage yawan ma'aikatan agajinta a Nijer, tare da takaita 'yan kalilan da ta kyale ma a birnin Yamai kadai, kuma domin kaucewa fadawa cikin rikici irin na Mali ne hukumomin Nijer suka ce suna tsaurara matakan tsaro da nufin tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma tsarin dimokradiyyar a kasar.

Mawallafi : Mösch, Thomas / Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani