1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Museveni zai sake tsayawa takara a zaben shugaban kasar Uganda a badi

November 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvKM

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ba da sanarwar cewa zai sake tsaya takara a zaben shugaban kasar da za´a yi a cikin shekara mai zuwa. Shugaban dai na son ya tsawaita wa´adin mulkinsa ne na shekaru 20. Masu sukan lamirin shugaban na zargin sa da zama wani dan kama karya. Sanarwar da shugaba Museveni ya bayar ta zo bayan an shafe mako guda ana tarzoma da tashe tashen hankula bayan da kame babban mai kalubalantar shugaban a wannan zabe Kizza Besigye. A ranar juma´a KTT ta bi sahun Amirka wajen nuna damuwa game da tsare Besigye. A farkon wannan shekara majalisar dokokin Uganda tare da gagarumin rinjaye ta kada kuri´ar soke tsohon tsarin da ya takaita wa´adin shugabanci, wanda da zai kawo karshen shugabancin Museveni.