1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi a Turai sun nesanta kansu daga harin Paris

Muhammad nasir AwalJanuary 8, 2015

Shugabannin Musulmi ciki da wajen kasar Faransa sun yi Allah wadai da harbe-harben, sannan sun mika ta'aziyyarsu ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu.

https://p.dw.com/p/1EHbX
Djelloul Seddiki und Joel Mergui
Hoto: AFP/Getty Images/T. Samson

Bayan harin da aka kai kan 'yan mujallar nan ta Charlie Hebdo a birnin Paris na kasar Faransa da kuma zanga-zangar da masu adawa da yaduwar addinin Musulunci ke yi kowace ranar Litinin a nan Jamus, kungiyoyin Musulmi na kara nuna damuwa game da kai musu hare-hare da kuma yi musu bita da kulli.

A martanin da suka mayar jim kadan bayan harin na ranar Laraba a birnin Paris da yayi sanadiyar mutuwar mutane 12, dukkan shugabannin addinin Musulunci a ciki da wajen kasar Faransa sun yi Allah wadai da harne-harben, sannan sun mika ta'aziyarsu ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu.

Trauer nach Anschlag auf Charlie Hebdo in Paris
Masu gangamin adawa da harinHoto: AFP/Getty Images/D. Meyer

A nan Jamus ma sun yi tir da harin. A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa game da ta'asar ta birnin Paris, Bekir Alboga, masanin kimiyyar addinin Musulunci kuma wakilin kungiyar Musulmin Turkiya da ke kula batutuwan addini a Jamus DITIB ya ce Musulunci addini na zaman lafiya kuma dole Musulmi a Jamus sun nuna a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya ce: "Nan-take tun ranar Laraba mun nesanta kanmu daga hari kuma mun yi tir da shi. Muna kira ga Jamusawa da su san cewa daukacin Musulmi a Jamus, 'yan kasa ne da ke mutunta kudin tsarin mulkin kasa kuma al'uma ce da ta saje da 'yan kasa da kuma ba ta da alaka da ayyukan ta'addanci na kasa da kasa. Hudubobi a cikin masallatayya na karfafa wannan matsayin cewa Musulunci addinin zaman lafiya ne da jin kai wanda ya zama wajibi ko wane Musulmi ya nuna."

Sake buga wani zanen batanci da mujallar ta Charlie Hebdo ta yi, shi ya janyo wannann harin da aka kai mata. Ko mene ne matsayin majalisar tsakiya ta Musulmin Jamus game da irin wadannan zane-zane na bandariya. Nurhan Soykan ita ce babbar sakatariya a majsalisaar ta Musulmin jamus wadda kua ke shiga tattaunawar neman fahimtar juna tsakanin addinai a ciki kasar.

Trauer nach Anschlag auf Charlie Hebdo in Nizza
Zaman makoki a FaransaHoto: AFP/Getty Images/V. Hache

Ta ce: "Ko shakka babu zanen bandariya abu ne da bai dace wajen bayyana ra'ayi. Dole ne a rika sara ana duban bakin gatari. Ko da yake wannan wani batu ne daban. Mun kanmu muna jure wa munanan abubuwa a kullum da ke ci mana tuwo a kwarya fiye da zanen bandariyar. Amma Annabinmu ya fuskanci munanan abubuwan fiye da mu kuma ya yi hakuri. Saboda haka ya kamata mu yi koyi da shi da kma irin hakuri da ya nuna."

Yanzu dai, kungiyoyin Musulmi a Jamus na nuna damuwa cewa bayan harin na Faransa da kuma jerin zanga-zangogin da masu adawa da yaduwar Musulunci a Turai wato Pegidav ke yi, ana iya samun karuwar hare-haren a kan Musulmi da kadarorinsu. Sai dai kungiyoyin sun yi fata al'umma za ta jure wa wannan zaman dar-dar.