1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmin Rohingya sun shige Bangaladash

August 28, 2017

Rahotanni daga Bangaladash, na cewa musulmi 'yan kabilar Rohingya kimanin dubu guda suka kutsa ta karfin tsiya, suka kuma shige cikin kasar a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/2izWy
Myanmar Kämpfe Flucht Rohingyas nach Bangladesch
Hoto: Getty Images/AFP/W. Moe

Rahotanni daga Bangaladash, na cewar musulmi 'yan kabilar Rohinga kimanin dubu guda suka kutsa ta karfin tsiya, suka kuma shige cikin kasar a wannan Litinin. 'Yan kabilar dai sun yi zaman kwanaki biyu a kan iyakar kasar ta Bangaladash, bayan guje wa rigima da 'yan Budha da ke a kasar Bama. Bayanai sun ce daruruwan mutanen sun fuskanci fushin dakarun kasar ta Bama ne, lokacin da wasu suka far wa shingen binciken jami'an tsaro a yammacin  kasar a karshen mako. Dakarun sun ce 'yan kabilar ta Rohinga sun arce ne lokacin da suka ji aman harbe-harben da  dakarun kasar Baman suka sako, yayin da suke iyakar kasar. Yanzu dai 'yan Rohingya dubu tara ne ke a cikin Bangaladesh tun da rigima ta barke tsakaninsu da 'yan tawayen kasar Bama.