1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 10 sun mutu a fashewar wani abu a Istanbul

Gazali Abdou tasawaJanuary 12, 2016

A Turkiyya wani abu da ya tarwatse a safiyar wannan talata a dandalin Sultanahmet na birnin Istanbul ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 a yayin da wasu 15 suka ji rauni.

https://p.dw.com/p/1HbrP
Türkei Explosion in Istanbul
Hoto: Reuters/O. Orsal

A Turkiyya Wani abu da ya tarwatse a safiyar wannan talata a dandalin Sultanahmet na birnin Istanbul ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 a yayin da wasu 15 suka ji rauni.

Shi dai wannan dandali na Sultanahmet wuri ne da ke a tsakiyar unguwannnin tarihi na birnin na Istanbul inda 'yan yawon buda ido na kasashen Turai ke yawan ziyarta.

Hukumar 'yan sanda kuma ta ce shaidun gani da ido sun ce an gano gawarwakin mutane kwankwance, da ma sassan jikunkunan mutanen a cikin filin wanda ke kusa da bulan masallaci da kuma cocin Sainte-Sophie.

Gidan talabijin na kasar ta Turkiyya na CNN ya ruwaito cewa akwai 'yan yawan buda ido 'yan kasashen Jamus da Norway daga cikin mutanen da suka ji rauni a cikin lamarin.

Gwamnan birnin na Istanbul ya bayyana cewa tuni suka soma gudanar da bincike domin tantance ko harin ta'addanci ne aka kawo ko kuma a a.

Sai dai tuni wasu kafofin yada labarai na kasar suka bayyana lamari da cewa harin kunar bakin wake ne aka kai.