1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asarar rayuka cikin fada da Boko Haram a N'Djamena

Gazali Abdou TasawaJune 29, 2015

'Yan sandar sun kai samame ne a wata unguwar kewayen N'Djamena da 'yan Boko Haram ke boye makamansu.

https://p.dw.com/p/1Fozm
Tschad Fahne Soldaten Kampf gegen Boko Haram Nigeria
Hoto: Reuters/Emmanuel Braun

A kasar Chadi manyan jami'an 'yan sanda biyar da kuma mayakan kungiyar Boko Haram shida sun hallaka a wannan Litinin lokacin wata bata kashi da ta hada bangarorin biyu lokacin wani samame da jami'an 'yan sandar suka kai a wata unguwar kewayen birnin N'Djamena da ake zargin maboyar makaman kungiyar ta Boko Haram ce.

Babban alkalin gwamnatin kasar ta Chadi Alghassim Khamiss wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce jami'an tsaron sun kai samamen ne a wani mataki na ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo mutanan da ke da hannu a cikin tagwayen hare-haren da kungiyar ta kai ran 15 ga wannan wata na Yuni a birnin na N'Djamena da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 34.

Hukumomin kasar ta Chadi sun ce sun yi nasarar kama tarin harsasai da dai sauran makamai masu tarwatsewa a lokacin samamen da jami'an tsaron suka kaddamar. A ranar Lahadin da ta gabata hukumomin kasar sun ce kawo yanzu sun kama mutane 60 da ake zargi da hannu a cikin hare-haren birnin N'Djamenar.