1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 17 sun mutu a rikicin Somalia

July 28, 2010

Gabzawa a tsakanin dakarun Somalia da masu tada zaune tsaye ya janyo mutuwar mutane 17

https://p.dw.com/p/OWpb
Hoto: AP

Tashe - tashen hankular da suka ɓarke a birnin Mogadishu na ƙasar Somalia a tsakanin masu tada ƙayar baya, da kuma dakarun gwamnatin Somaliar da ke samun goyon bayan ƙungiyar tarayyar Afirka, ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla fararen hula 17.

A cewar shugaban sashen ɗaukar marasa lafiya a birnin Mogadishu Ali Musa, bayan gawarwakin mutane 10n da suka ɗeba, akwai kuma mutane 46n da suka sami rauni. Ali Musa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, bakwai daga cikin waɗanda suka sami raunin ne suka cika a asibiti, a yayin da sauran kuma ke ci gaba da karɓar magani a asibitin Madina dake birnin na Mogadishu.

A halin da ake ciki kuma wani ƙwararre akan lamuran da suka shafi ƙasar Somalia, Rodga Middleton, ya ce bai kamata al'ummomin ƙasa da ƙasa suyi gaggawar yin murna game da alƙawarin tura ƙarin dakarun da tareon shugabannin Afirka na AU ya yi ba:

" Akwai buƙatar Majalisar Ɗinkin Duniya ta tantance wannan batun, da kuma zauren babban taron ƙungiyar tarayyar Afirka. Saboda haka babu wani ci gaban a zo a ganin da za'a samu gabannin isowar waɗannan sojojin. A baya kuma mun ga lokutan da ƙasashe suka yi alƙawarin tura dakaru ga rundunar ƙungiyar tarayyar Afirkar da ke aiki a ƙasar Sonaliya, amma kuma hakan bai afku ba. Saboda haka ko dai za'a bi faɗi da cikawa a wannan karon, lokaci ne kawai zai nuna."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu