1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 36 sun rasa rayukansu a tashe-tashen hankulla a Iraqi.

June 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buu7

A halin da ake ciki a Iraqin dai, a ƙalla mutane 36 ne rahotanni suka ce sun rasa rayukansu a ci gaban tashe-tashen hankullan da ake ta yi a ƙasar. Wasu jerin bamabamai da aka ta da a cikin motoci sun janyo asarar rayukan mutane 18 a garin Kirkuk da ke arewacin ƙasar. A birnin Bagadaza kuma, wani bam da aka tayar kusa da motar sintirin ’yan sanda, ya halakad da ɗan sanda ɗaya da kuma wani fursunan da suuke ɗauke da shi a motar, sa’annan jami’an ’yan sandan 4 ne suka ji rauni. A wani harin rokoki a kudancin birnin kuma, mutum ɗaya ne ya sheƙa lahira, sa’annan wasu 12 suka ji raunuka.

A duk faɗin Iraqin kuma, rahotanni sun ce a ƙalla, mutane 16 ne suka rasa rayukansu a jerin buɗe wuta da hare-haren bamabamai da aka kai. Waɗannan tashe-tashenj hankullan dai sun biyo bayan wata sanarwar da gwamnatin ƙasar ta bayar ne na ɗaukan tsauraran matakan tsaro, inda aka zuba dakarun Amirka da na Iraqin, fiye da dubu 70, don su gudanad da wani ɗauki na fatattakar ’yan yaƙin gwagwarmaya daga birnin.