1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam a wani masallaci a Kamaru

Yusuf BalaJanuary 13, 2016

Wannan tashin abin fashewar dai ya faru ne lokacin sallar Asubahi a wani masallaci a kauyen Kouyape na Kolofata.

https://p.dw.com/p/1HcPa
Kamerun Kolofata Selbstmordanschlag Soldaten
Wurin da aka kai hari a yankin Kolofata na KamaruHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Wani dan kunar bakin wake ya halaka masallata 12 a wani masallaci a Arewacin Kamaru a ranar Laraban nan kamar yadda jami'an tsaro suka bayyana, harin da ya faru a yankin da ke ganin irin wannan tashin hankali sakamakon ta'addancin Boko Haram daga lokaci zuwa lokaci.

Wannan tashin abin fashewar dai ya faru ne lokacin sallar Asubahi a wani masallaci a kauyen Kouyape na Kolofata daga Arewacin kasar ta Kamaru kusa da iyaka da Najeriya inda a nan take mutane sha daya suka rasu na sha biyun ya rasu ne bayan an garzaya da shi asibiti kamar yadda majiyar jami'an tsaron ta nunar.

Tun dai daga tawan Yulin shekarar bara ne yankin Arewa mai nisa na Kamaru ke ganin hare-hare da ake kaiwa daga lokaci zuwa lokaci wanda kungiyar Boko Haram me ikirarin mubayi'a ga mayakan ta'addancin IS ke daukar nauyin kaiwa.