1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun mutu a Diffa

August 24, 2019

Rahotannin da ke fitowa daga Jamhuriyar Nijar, sun ce wani hari da ake zargin mayakan Boko Haram da kaiwa, ya halaka akalla mutum 12 a yankin kudu maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3ORM2
Boko Haram
Hoto: Java

Maharan sun kai harin ne cikin daren da ya gabata a gundumar Gueskerou na yankin Diffa, yankin kuma da ke fama da hare-haren da kuma garkuwa da mutane.

Shaidu sun ce 11 daga cikin wadanda suka mutun, an kashe su ne da tsinin bindiga.

Ko cikin watan Maris da ya gabata ma wani harin ya yi sanadin mutuwar fararen hula takwas da kuma jami'an 'yan sanda bakwai.

Kungiyar Boko Haram mai fafutukar kafa daula ta halaka sama da mutum dubu 27 a Najeriya kadai.