1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matslolin cutar shan Inna

Tanko Bala, AbdullahiNovember 13, 2008

Yaƙi da cutar Polio a Nijeriya da Niger.

https://p.dw.com/p/FtEV
Allura rigakafin ƙananan yara kan cutar PolioHoto: AP Photo

Cutar shan inna cuta ce mai yaɗuwa musamman a tsakanin ƙananan yara. Yaƙi da cutar shan inna ko kuma Polio ya kasance babban ƙalubale dake fuskantar hukumomi musamman a Nigeria.

Bayanai na ƙungiyar lafiya ta duniya ya nuna cewa ƙasashe huɗu ne suka kawai saura a duniya baki ɗaya waɗanda har yanzu cutar ta Polio ke cigaba da yaɗuwa a cikin su. Waɗannan ƙasashe kuwa sun haɗa da Nijeriya da Indiya da Pakistan da kuma Afghanistan.

A Nigeria alal misali bayanan ƙungiyar lafiya ta duniya yace a farkon watanni bakwai na wannan shekarar, an sami rahoton sabbin kamuwa da cutar Polio musamman a arewacin Nijeriya. Ganin haka ya sa gwamnatin tarayyar Nigeriyar ta ƙaddamar da gagarumin shirin Allurar rigakafin shan innan a faɗin ƙasar.


Sai dai kuma duk da wannan yunƙuri wasu jamaá har yanzu suna ɗari-ɗari da shirin Allurar rigakafin walau dai saboda jahilci ko kuma rashin fahimtar faídarsa kamar yadda Madam Ruth Abwo jamiár wayar da kan jamaá game Polio a jihar Plato ta nunar.


Akwai hukumomi na ƙasashen waje kamar ƙungiyar lafiya ta duniya da asusun kula da ƙananan yara ta Majalisar dinkin duniya UNICEF da sauran su waɗanda ke bada gudunmawa game da Allurar. Ruth Abwo tace sun gamsu kwarai da taimakon da waɗannan ƙungiyoyi ke bayarwa wajen yaƙi da cutar shan inna a jihar Plato.

Ƙwayar cutar Polio tana yaɗuwa ne ta hanyar gurɓataccen abinci ko ruwan sha mara tsabta. A yayin da yaro yaci abinci ko ya sha ruwa wanda ke ɗauke da ƙwayar cutar, to kan cigaba da hayayyafa a cikin hanjin sa inda daga nan kuma ta kan mamaye jijijoyin jikin sa.

Alamun farko da cutar ke nunawa sun haɗa da zazzabi da kasala da ciwon kai da Amai da kuma ƙagewar wuya sannan da ciwon gaɓoɓi wanda idan baá ankara ba ta kan kai ga shanyewar ƙafafuwan yaro. Hanya kaɗai da zaá iya kare aukuwar hakan ita ce ta yin Allurar rigakafi.

A cewar Turakin Jos Alhaji Inuwa Ali, sakamakon yadda wasu jamaá suke nuna tsoro ko shakku game da rigakafin yasa sarakuna gargajiya a matsayinsu na shugabannin alúma suke jan hankali ga talakawansu domin wayar musu da kai su bada goyon baya ga shirin rigakafin.

Matukar zaá sami yaro ɗaya yana ɗauke da ƙwayar cutar to kuwa yana iya shafar sauran yara na maƙota a gida ko a gari baki ɗaya. Rueben Gorip wani magidanci a jihar Plato yace iyaye suna da muhimmiyar rawa da zasu taka a wannan fannin wajen kare lafiyar`yaýansu cewa yayi.

Yayin da wasu jamaár ke ganin gwamnatoci basu himmatu sosai ba wajen kawar da wannan cuta Rueben na da raáyin cewa na bakin ƙoƙari sai dai idan Dambu yayi yawa baya jin mai.

A cewar ƙungiyar lafiya ta duniya a dukkan ƙasashen Afirka, Nijriya ce kaɗai ke da cutar Polio a halin yanzu. A saboda haka ƙasashe waɗanda ke maƙwabtaka da Nijeriya suke ɗaukar matakai domin kare shigar da cutar a cikin ƙasashensu.Wannan dalili ne ma yasa hukumomin lafiya su kan gudanar da aikin haɗin gwiwa a lokacin rigakafin a yankunan kan iyaka musamman a tsakanin Nijeriya da Niger.

Masu magana kan ce dai hannu ɗaya baya ɗaukar jinka, akwai buƙatar haɗa hannu wuri guda domin yaƙi da wannan cuta ta Polio wadda bata da magani sai dai rigakafi.