Dan bindigar Christchurch ya amsa laifinsa
March 26, 2020Talla
A zaman shari'ar da ake yi na kisan gilla a garin Christchurch na kasar New Zealand, ba zato ba tsammani mutumin da ake tuhuma dan kasar Australiya ya amsa laifinsa.
Kamar yadda 'yan sanda suka nunar mutumin ya amsa laifin hallaka mutane 51. A shekarar 2019 aka harbe mutane har lahira a hare-haren da dan bindigar ya kai kan masallatai biyu a Christchurch. Maharin ya dauki bidiyon ta'asar ya kuma wallafa a intanet.
Gabanin ya kai harin dan bindigar mai shekaru 29, ya wallafa kalaman wariya a intanet. Ana kuma zarginsa da aikata ta'addanci.
Yanzu haka ana tsare da shi a wani kurkuku da ke birnin Auckland, mai nisan sama da kilomita 1000 arewa da garin Christchurch.