1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure na ci gaba da mutuwa a teku

Andreas Noll/ Suleiman BabayoFebruary 11, 2015

Kusan bakin haure 30 suka hallaka a gabar ruwan Italiya, lokacin da suka samu hadari bayan tasowa daga Libiya, kamar yadda aka tabbatar.

https://p.dw.com/p/1EZVD
Symbolbild afrikanische Flüchtlinge im Mittelmeer
Hoto: picture-alliance/Milestone Media

Bakin hauren sun kira masu gadin-gabar tekun Italiya lokacin faruwar hadarin da ya hallaka mutane 29. Masu gadin tekun sun yi tafiya mai nisan kilo-mita 160, inda suka samu nasarar ceto mutane 105 da rai. Galibin bakin hauren sun fi daga yankin kudu da Saharar Afirka domin samun kyakkyawar makomar rayuwa a kasashen Turai. An kai wadanda suka samu raunika zuwa asibitin Sicily saboda samun magani. Ranar Lahadi da rana masu-gadin tekun suka samu kira daga bakin hauren da ke cikin mawuyacin hali.

Philippo Marini ke zama kakakin hukumar gadin-gabar tekun ta kasar Italiya yayi tsokaci:

"Igiyar ruwa ta tashi da tsawon kimanin mita takwas zuwa tara, dauke da iska mai karfi. Yanayi ne mai wuya. akai dauki daga Lampedusa domin namu jiragen sai sun jure kafin aka kai dauki wa bakin haure 105 a kusa da gabar tekun Libiya. An ceto mutanen da suke cikin jirgin ruwa."

Verstorbene Flüchtlinge im Hafen von Lampedusa
Hoto: Reuters/Vista via Reuters TV

Fiye da bakin haure 3,200 suka rasa rayukansu a yunkurin shiga Turai daga arewacin Afirka ta amfani da kananan jiragen ruwa a shekarar da ta gabata ta 2014. Yanzu masu fataucin mutanen sun fara amfani da manyan jiragen ruwa inda suke makare mutane bayan karbar makudan kudade.

"Giusi Nicolini shugaban hukumar gudanarwar birnin tsibirin Lampedusa wadda ta nuna takaici kan kawo karshen ayyukan ceton gaggawa na bakin haure, wanda aka yi a watan Oktaba da ya gabata. Ta bayyana cewa yanzu bakin haure da suka shiga halin ha'ula'i suna kiran hukumominsu kai tsaye maimakon masu gadin-gabanr ruwa na kasashen Turai:

Verstorbene Flüchtlinge im Hafen von Lampedusa
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Buccarello

"An daina aikin da shirin ceto na ko-ta-kwana, wanda yanzu ake yi ba jinkai ba ne. Yanzu masu aikin gabar ruwan tekun Turai ne suke aiki. Lokacin da lamarin ya faru bakin hauren da kansu mu suka kira saboda neman taimako."

"A hukumance an ceto fiye da bakin haure fiye da 100,000 bayan kafa hukumar ceton gaggawar. Lamarin ceton bakin hauren da ke yunkurin shiga Turai na cin makudan kudade. Kafin kawo karshen aiki a watan Oktoba, ana amfani da kudaden harajin Italiyawa kimanin Euro milyan 10 kowane wata, inda yanzu aka maye tsarin da mai saukin tafiyarwa wajen kashe kudade.

Mission Mare Nostrum Italien Flüchtlinge Rettung Mittelmeer 2014
Hoto: picture-alliance/dpa/Giuseppe Lami

A cewar shugabar hukumar gudanarwar tsibirin Lampedusa yanzu sun shiga mawuyacin hali:

"Mun dauka cewa kasashen Turai sun kai mu sun baro"

'Yan siyasa a Italiya kan tabka mahawara bisa yadda za a ceci bakin hauren ganin cewa mafi yawa kan mutu saboda sanyi, amma ba domin jirgin ruwa da ya tarwatse a cikin teku ba.