1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta kashe mutun na farko a Madagaska

Gazali Abdou Tasawa
May 17, 2020

A Madagaska, an samu mutun na farko da ya mutu a sakamakon cutar Covid 19, kusan watanni uku bayan billar cutar a kasar inda kawo yanzu ta harbi mutane 304.

https://p.dw.com/p/3cMqs
Somalia Mogadischu Todesopfer von Covid-19
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F.A. Warsameh

Hukumar yaki da annobar Corona a kasar Madagaska ta ce mutumin farkon da cutar corona ta kashe a kasar wani mutum ne dan shekaru 57 da ake aikin gadi a gidan asibiti na garin Toamasina da ke a gabashin kasar. Kuma ya rasu ne a yammacin ranar Asabar da cutar ta Covid 19 baya ga fama da ciwon siga da na hawan jini da yake yi.

Ya zuwa wannan Lahadi dai mutane 304 ne suka harbu da cutar ta Covid 19 a kasar ta Madagaska wacce ta kasance a kanun labarun kafafan duniya bayan da ta kaddamar da wani maganin gargajiya na yaki da cutar ta Covid 19 wanda aka sarrafa da kunnuwan itaciyar tazargade ko kuma Artemesia a Turance, maganin da amma Hukumar lafiya ta Duniya ta yi gargadi shugabannin Afirka kan amfani da shi tana mai cewa ba a gudanar da gwajin kimiyya na tabbatar da ingancinsa ba.