1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar jakadan kasar Palasdinu

January 1, 2014

Rundunar 'yan sanda a Jamhuriyar Chek ta sanar da rasuwar jakadan Palasdinu a kasar Jamal al-Jamal, biyo bayan fashewar wani bom a gidansa dake Parague.

https://p.dw.com/p/1Ak6a
Hoto: picture-alliance/AP

Ma'aikatar harkokin waje ta Palasduinun dai ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace bom din ya tashi ne jim kadan bayan da Al-Jamal ya bude asusun ajiyarsa na cikin gida. Rahotannin sun bayyana cewa Al-Jamal me kimanin shekaru 56 a duniya, ya rasu ne bayan da aka garzaya da shi asibitin sojojin kasar sakamakon munanan raunukan da ya samu, sai dai daga bisani rai yayi halinsa.

Jamal al-Jamal dai ya karbi ragamara jakadanicin Palasdinu a Jamhuriyar Cek din ne a watan Oktoban da ya gabata, yayin da kuma kwananki kalilan kenan da tare a gidan nasa. Tuni dai hukumomin kasar ta Palasdinu suka sanar da tura jami'ai domin su shiga cikin binciken musabbabin fashewar bom din da takwarorinsu na Jamhuriyar Cek din keyi. Kawo yanzu dai jami'an tsaron Jamhuriyar Cek din sun sanar da cewa babu wata shaida dake nuni da cewa harin ta'addanci aka kaiwa Al-Jamal din.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu.