1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar sojojin Chadi a Arewacin Mali

February 23, 2013

Dakarun Chadi 13 ne suka rasa rayukansu akan iyakar Mali da Aljeriya lokacin da suka fafata da masu kaifin kishin addini. Hukumomin Ndjamena ne suka bayar da wannan sanarwa.

https://p.dw.com/p/17kW0
Hoto: Picture-Alliance /dpa

Gwamnatin Chadi ta baiyana cewa sojojinta 13 da kuma 'yan bindiga 65 sun rasa rayukansu, lokacin da suka gwabza kazamin fada tsakaninsu a cikin tsaunukan arewacin Mali da ke kan iyaka da Aljeriya. Dakarun kasar ta Chadi dubu biyu da kuma na wasu kasashen Afirka ne dai, suke maye gurbin takwarorinsu na Faransa sannu a hankali, wadanda ke kubatar da arewacin kasar ta Mali daga hannun masu kaifin kishin islama.

Ita dai Faransa da ta yi wa Mali mulkin mallaka ta kutsa kasar ne da nufin ja wa masu kaifin kishin addini birki, a yunkurin da suka yi na mamaye kudancin kasar baya ga arewaci da a wancan lokaci ke hannunsu. Sai dai rahotonnin da ke zuwa mana da birnin Gao sun nunar da cewa abzunawa tsaffin 'yan tawaye sun fuskanci harin kunar bakin wake daga bangaren masu tsattsauran ra'ayin addini inda mutane biyar suka rasa rayukansu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi