1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Na'aurar nadar magana ta Germanwings

Mohammad Nasiru AwalApril 2, 2015

An gano na'urar nadar magana ta biyu ta jirgin Germanwings da ya yi hatsari a Faransa kuma mutane 150 da ke ciki suka mutu.

https://p.dw.com/p/1F2DC
Germanwings Airbus A320 Black-box
Hoto: Reuters/BEA

Masu shigar da kara a birnin Marseille na kasar Faransa sun ce ma'aikatan ceto sun gano na'urar nadar magana ta biyu ta jirgin saman Germanwings da ya fadi a yankin tsaununkan kasar Faransa makon da ya gabata. Na'urar za ta ba da karin bayani game da tafiyar jirgin saman samfurin Airbus A320. Tun a ranar da jirgin ya fado aka gano na'urar nadar maganar ta farko, wadda bisa abubuwan da aka ji, mataimakin matukin jirgin saman ya rufe kaftin din a wajen dakin matuka, sannan da gangan ya yi setin jirgin ya fadi, ya halaka dukkan mutane 150 da ke cikinsa.