1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Adawa da mayar da shugaban NHIS

Uwais Abubakar Idris
February 12, 2018

Hukumar kula da Inshorar lafiya ta Najeriya NHIS ta bayyana damuwa a kan koma bayan da ake fuskanta a harkar inshora shekaru 13 da fara aiwatar da shirin.

https://p.dw.com/p/2sYUb
Nigeria | Krankenhaus in Abuja
Daya daga cikin asibitoci dake bayar da inshorar lafiya a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Korafin hukumar kula da inshorar lafiya NHIS  na zuwa ne a  daidai lokacin da ake takaddama a kan  matakin shugaban kasar Muhammadu Buhari na sake mayar da shugaban hukumar Farfesa Usman Yusuf a bakin aikinsa, watanni bakwai da dakatar da shi bisa zargin cin hanci da rashawa.

Tun bayan bankado batun rashawar ake ta cece-ku-ce kan makomar hukumar da ake zargi da nuna gazawa a harkokinta na kulawa da miliyoyin mara lafiya. A taron ‘yan jaridu da ya gudana a ranar Litinin a Abuja fadar gwamnatin kasar, shugabanin hukumar sun yi kokari na bayyana zahirin halin da ake ciki a kan batun inshorara lafiya ta Najeriya da yanzu shekaru 13 da kafa wa.  

Yanzu dai ta kai ga an girke jami’an tsaro a kofar shiga hukumar domin kaucewa dauki ba dadi na kungoyin ma’aikata da ke nuna adawa da maida shugaban hukumar a bakin akinsa. Tun kafin wannan lokaci  majalisar wakilan Najeriya ta bayyana cewa dole ne a mayar da shugaban a bakin aikinsa.

Najeriya na matukar bukatar zaburar da aikin hukumar samar da inshorar lafiya ta kasar, abin da kwararu ke bayyana zai iya tasirin wajen kyautata samar da lafiyar jama’a.