1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar hakkin yara a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
December 10, 2019

A daidai lokacin da ake bikin ranar kare hakkin dan Adam a duniya baki daya, a Najeriya wasu kungiyoyi ne suka yi zanga-zangar lumana domin neman jihohin kasar su sanya hannu kan dokar kare hakokkin yara.

https://p.dw.com/p/3UY3e
Südafrika Kapstadt Menschen 2018 Township LANGA Kindertreffpunkt Kapstadt Township Langa *** S
Kokarin tabbatar da dokar kare 'yancin yaraHoto: imago/W. Schmitt

Tun dai tsawon shekaru 30 din da suka gabata ne aka kafa dokar kare hakkin kananan yaran a Najeriya, sai dai har yanzu wasu jihohin na jan kafa wajen aiwatar da ita, duk kuwa da karuwa cin zarafin yara kanana a kasar. Wadannan kungiyoyi da suka yi zanga-zangar ta lumana sun bayyana bacin rai da damuwa a kan abin da suka kira ta'zzarar take hakokin yara kanana da cin zarafinsu a Najeriyar musamman a yankin arewacin kasar, inda a can ne har yanzu akwai jihohin da suka ki sanya hannu a kan wannan doka.

Karikatur: Nigeria Kinderrechte
Yara na bukatar 'yancinsu a NajeriyaHoto: DW/Baba

An dai jima da amincewa da ita da aka yi a matakin tarayya, sai dai har yanzu jihohi da dama ba su amince da ita ba, abin kuma da za a iya cewa jan kafar jihohin ke yi na bayar da kafa ga masu take hakki da cin zarafin yaran. Ana dai wannan ne a dai lokacin da ake nuna damuwa kan karuwar take hakokin dan Adam a Najeriyar, batun da ke zaman babban lamari musamman yadda hatta yara kanana basu tsira ba da masu aikata wannan mummunar dabi'a da rashin aiwatar da hukunci mai tsauri ke bayar da kafa ta ci gaba da aikatawa.