1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murna da karin albashin a Najeriya

Uwais Abubakar Idris AMA
October 18, 2019

Ma’aikatan gwamnati na cikin murna da farin ciki sakamakon kulla wata yarjejeniyar karin kudaden albashi tsakanin 'yan kwadago da wakilan gwamnatin tarayyar Najeriya bayan shafe tsawon lokaci ana ta takkadama.

https://p.dw.com/p/3RXWD
Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010
Hoton wani gangamin ma'aikatan kwadago a Najeriya a 2010Hoto: dapd

Bayan kwashe watanni ana tattaunawa da ta kai ga barazanar yajin aiki da gamaiyyar kungiyon kwadagon suka yi, a karshe dai an cimma yarjejeniya kan tsari na aiwatar da sabon albashi ga ma’aikatan gwamnatin Najeriyar. Tsarin ya tashi tun daga mataki na daya har zuwa na 17 kowane da adadin kason da aka kara mashi.

A yayin wata hira da tashar DW, Sanata Chris Ngige da ke zaman ministan kwadago da ingantuwar aiki na Najeriyar ya ce "mun amince da karin albashin na ma’iakaci mafi kankanta da ke mataki na daya na Naira dubu 30, amma ma’aikatan da ke mataki na bakwai an yi musu karin kaso 23, mataki na takwas an masu karin kaso 20, wadanda ke ajin mataki na tara kuma kashi 23, sai mataki na 10 zuwa 14 an ware masu kaso 16 yayin da ma’aikatan da ke mataki na 15 zuwa 17 suka samu kari na kashi 14."

A share daya an yi karin kaso hudu ga ma’aikatan gwamnati da na sashin kiyon lafiya, da malaman makaranta da masu bincike, haka kuma sojoji da sauran jami'an tsaro, matakin da ya sha guda daga ma'aikatan dabam-dabam na kasar.

Tuni kungiyoyin kwadagon kasar suka nuna gamsuwa da karin albashin bayan barazanar da suna nuna tun daga farko na ficewa zauren tattaunawa sai dai masana na ganin cewar matakin karin albashi bai kamata ya dinga kasancewa abin ja in ja ba tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago a Najeriya a yayin da karin albashin ya sanya mutane da dama nuna fargaba na hauhawar farashin kayayakin masarufi a fadin kasar.