1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Baa kyautata wa malaman makaranta

October 5, 2016

Biyar ga watan Oktoba rana ce da MDD ta ware don nazarain halin da malaman makaranta ke ciki da nufin kyautata rayuwarsu.

https://p.dw.com/p/2Qtcl
Nigeria Studenten in Jos
Hoto: picture-alliance/epa/Ruth McDowall


Malaman makarantu na taka muhimmiyar rawa wajen koyar da ilimi da tarbiya yara sai dai kuma a wannan sashei na duniya su na cikin masu fama da Kuncin da kuma barazana na rayuwar musamman yadda aka samu Kungiyar da ke yaki da karatun Boko a Najeriya.


Rahoton kwanan nan da wasu kungiyoyin jin kai na kasa da kasa wato "The 21st Century Wilberforce Initiative" da "Stefanus Foundation" suka fitar, ya nuna cewa akwai malamai makarantun Boko guda 611 da suka hallaka a rikicin Boko Haram, kana wasu malamai dubu 19 suka rasa matsugunensu.

Liberia Universität lässt 25.000 Studenten durchfallen
Hoto: picture-alliance/dpa


Yanayin tabarbarewar tsaron ya shafi harkokin rayuwa na malamai da dama inda wasu ala tilas suka yi watsi da aikin, wasu kuma su ka rasa nutuswar da ake bukata domin koyarwa abin da ake ganin ya shafi koyarwar da ake yiwa dalibai.


Malam Muhammad Ibrahim malami ne a wata makarantar sakanadaren kimiyya da ke Gujuba a jihar Yobe ya yi bayanin irin halin da suka samu kansu a ciki, sanadiyyar tabarbarewar tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.


A cewar Hauwa Ibrahim Jauro, malama a makarantar sakandare da ke Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe, a baya sun sha fama da fargaba amma yanzu an samu sauki kuma komai ya fara komawa yadda yake baya.

Jake Epelle
Hoto: Nonye Aghaji


Wannan yanayi na Malami haka ya ke a kusan dukkanin jihohin Borno da Adamawa da Taraba da Bauchi da Gombe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya sai dai wani wuri ya fi wani tsanani.


Yanzu haka kuma matsatsin tattalin arzikin kasa da ake fama da shi yanzu a Najeriya ya kara jefa yawancin malami cikin mawuyacin hali saboda albashin su baya isa inda wasu wuraren ma ake fito na fito da kafin malaman su samu albashin.