1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya gabatar da nasarorin da ya cimma

November 17, 2017

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jerin nasarorin da gwamnatin kasar karkashin jagorancinsa ta cimma daga lokacin da ya hau kan karagar mulki a shekarar 2015 zuwa wannan lokacin.

https://p.dw.com/p/2nlXM
Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Shugaban na Najeriya ya yi bitar wadannan nasarori ne gaban dumbin magoya baya da makusanta a babban birnin tarayyar kasar Abuja inda ya tabo batutuwan da suka hada da tsaro musamman ma dai yaki da ta'addanci a sassan kasar daban-daban ciki kuwa har da yankin arewa maso gabas wanda rikicin Boko Haram ya tagayyara. Gwamnatin ta Buhari dai ta ce ta samu nasarar dakile aiyyukan ta'addanci a Najeriya da kusan kashi 80 cikin 100 daga hawanta kawo yau.

Nigeria Armee Soldaten
Tabbatar da tsaro na daya daga cikin irin abubuwan da gwamnatin Buhari ta ce ta yi daga hawanta mulki zuwa yauHoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

Baya ga batun tsaro, shugaban ya kuma tabo yakin da gwamnatinsa ta daura da cin hanci da rashawa wanda 'yan kasar da dama ke kallo a matsayin matsalar da ta dabaibaye kasar shekara da shekaru. Wannan batu na daga cikin irin abubuwan da ke sahun gaba a cikin jerin alkawuran da da jam'iyyar Buharin ta APC ta yi a lokacin da ta ke yakin neman.

Wani abu har wa yau da shugaban ya tabo shi ne tattalin arziki inda gwamnatinsa ta ce ta taka rawa ta a zo a gani wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya din daga irin halin kunci da ya samu kansa a ciki. Yayin bitar wadannan abubuwa dai, Buharin da jama'arsa sun yi kaddamar da wani littafin da ke dauke da jeri cigaban da suke ce sun samu a watanni kusan 30  da suka shafe suna jan ragamar kasar.