1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bukatar fahimtar juna a tsakanin musulmi

Uwais Abubakar Idris
April 24, 2019

​​​​​​​A ci gaba da kokarin samun fahimtar juna tsakanin mabiya dariku na addinin Musulunci, cibiyar daidaita mabiya addinai ta bukaci malamai masu wa'azi su kaucewa kalamai masu tada hankali.

https://p.dw.com/p/3HNAu
Islam in Nigeria
Hoto: DW/Katrin Gänsler

Wannan kokari na samun fahimtar juna a tsakanin mabiya darikun addinin musulunci a Najeriyar, ya taso ne saboda yawaitar furta kalamai na tunzuri ko batanci da sunan addini, lamarin da ke zama matsala ta cikin gida. Cibiyar daidaita mabiya addinan Musulunci da Krista da ke Kaduna wadda ta shirya taron, ta bayyana muhimmancin hadin kai a tsakanin mabiya darikun Izala, Darika da kuma Shi’a domin dorewar zaman lumana da fahimtar juna.

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi na daya daga cikin malaman da suka halarci taron ya jaddada bukatar zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai musamman a tsakanin musulmi kasancewar kowace darika mutum ya ke dukkaninsu sun yi Imani da kalmar Shahada.

Shi ma Dr Ishaq Yunus na kungiyar Izala yace haduwa da tattaunawa a tsakanin juna lamari ne da zai karfafa fahimtar a tsakanin juna. Mahalarta taron sun amince cewa samun fahimtar juna a tsakanin mabiya addinin musulunci zai taimaka wajen dinke baraka da kyautata muamala da fahimtar juna musamman a tsakanin su a dai lokacin da ake fuskantar watan azumin Ramadan da ake samun karuwar wa’azi na musulunci a kasar.