1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Wa'adin mika sunyen 'yan takara

Uwais Abubakar Idris AS
October 19, 2018

Wa'adin da hukumar zabe ta diba wa jam'iyyun siyasu na su mika 'yan takarasu na 'yan majalisun tarayya da na shugaban kasa ya cika a daren ranar Alhamis din da ta gabata sai dai an yi ta kai-komo kafin cikar wa'adin.

https://p.dw.com/p/36qK5
Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Wannan wa'adi da hukumar zaben ta tsara na cikin kaidojin da ke kunshe a jadawalin da ta fitar na shirye-shiryen gudanar da zaben na Najeriya da za'a a yi a shekara mai zuwa. Wannan dai ya sanya wakilan jam'iyyun da suka gudanar da zaben fidda gwani yin rige-rige na cika ka'idar.

Duk da cewa  lokacin da hukumar ta diba ya cika a sha biyun daren Alhamis 18 ga watan nan amma har zuwa safiyar ranar Juma'a mutane na kan layi don mika nasu sunayen ‘yan takara a dakin taro na kasa da kasa. Wakilin DW a Abuja Uwais Abubakar Idris ya ce an girke jami'an tsaro don tabbatar da tsaro.

Ko da yake da sauran lokacin ga wa'adin mika sunayen 'yan takarar gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi, ko akwai wani sauyi da aka samu a game  da batun ‘yan takara gwamna na jamiyyar APC a jiharZamfara? Tambayar kenan da DW ta yi wa hukumar zaben inda ta ce har yanzu tana kan bakanta na cewar za a yi zaben ba tare da 'yan takara na jam'iyyar APC a zamfara ba tunda ba su yi zaben fidda gwani ba.