1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cuwa-cuwa a batun gina sabon birni

Ubale Musa/GATAugust 28, 2015

Sama da hekta 3000 na fili mai tsada ne dai wasu yan kasuwar kasar suka diba da sunan gina sabon birnin zamani a cikin Abuja, batun da ke neman ya zamo na 'yan matan amarya.

https://p.dw.com/p/1GNes
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Sama da hekta 3000 na fili mai tsada ne dai wasu yan kasuwar kasar suka diba da sunan gina sabon birnin zamani a cikin Abuja. Birnin kuma da a cewar masu shi din zai samu gine-gine na dala miliyan dubu 18.500 ko kuma kasafin kudin kasar na shekara guda . Sannan kuma zai samar da ayyuka na kai tsaye har 250,000, banda wasu dubu 100,000 a harkar gine-gine.

To sai dai kuma sama da shekara bayan kadammar da shi birnin na neman komawa na aljanun da ba kowa a cikinsa dama kila hanyar wasoson filiyen talakawan birnin.

Babu dai ko da bulo guda da sunan gina sabon birnin har yanzu sannan kuma ga rikicin da ya mammaye malakin birnin da aka tsara zai zamo na biyu mafi girma a duniya bayan wani irinsa a kasar Koriya ta Kudu.

Duk da cewar dai a fadar shugaban kamfanin , wasu 'yan kasuwa 40 a ciki da wajen kasar ta Najeriya ne suka tsara jarinsu kaco kam domin gina birnin, a cikin tsakiyar rikicin dai na zaman tsohon sakataren gwamnatin kasar Anyim Pius Anyim da wasu kamfanoni biyu basic stack limited da kuma Company first limited da ake ta'allakawa da shi kansa.

Ana zargin wasu kamfanoni da wasu mutane a badakalar

Nigeria National Petroleum Corporation Öl-Industrie Korruption
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Tuni dai wani jami'in jam'iyyar PDP da mulki kasar yayin kaddamar da sabon aikin ya aike da wasika ta korafi ga shugaban dake kai yanzu da a cikinsa yake zargi Anyim din da damfarar kasar domin son ransa.

Ko bayan batu na mallakin daukacin filin ginin birnin dai ana kuma zargin Anyim din da samun yafiyar haraji na gwamnatin da ya kai Naira Miliyan dubu daya da dari biyu.

Abun kuma da ya tilasa shugaban kasar sammaci ga kamfanin na centenary City Plc da kuma abokan burin na Eagles Hills dake Daular larabawa domin ji daga bakinsu.

Mutanen da kamfanonin da ake zargi sun kare kansu

Bayan kamalla ganawar tasu dai shugaban kamfani Odenigwe Ike Micheal yace ba su abun boyewa a cikin harkokin kamfanin da yake jagoranta.

"Shugaban kasa ya na farin ciki da mu. Abokan huldar mu suna nan kuma basu tafi ba. Ga masu tunanin ba abun dake faruwa ku bi hanyar airport zaku ga injunanmu na aiki babu dare ba rana, game da batun tsohon sakataren gwamnati, ba zamu maida martani kan jita jita ba. In ta fito fili za mu maida martanin da ya dace"

Haus-Einsturz in Abuja
Hoto: DW

to sai dai ko ya zuwa yaushe mashinan na kamfanin ke iya fara fitar da ofisoshi da gidajen masu hannu a cikin shuni dai ita kanta sanarwar fadar gwamnatin kasar ta ce damuwarta zuwa yanzu na zaman hakkin mutanen da kamfanin ke kokarin sake tsugunarwar wa.

Sanarwar dai ta ce Shugaba Buhari zai bi diddigin aiki na kamfanin domin tabbatar da abun da ke faruwa a cikinsa.

Shi ma dai kamfanin na Eagles Hills ya ce ya gamsu da jarinsu cikin kasar ta Najeriyar duk da kace-nacen da ke kasa a fadar Mr Jamil Shargil dake zaman daya a cikin manyan darektocinsa.

"Mun yi bincikenmu a matsayin masu zuba jari kuma mun gamsu da sakamakon. Ba zamu yi bincike a kan jita jita ba. Zamu yi bincike a kan sahihai na bayanai , kuma mun tabbatar da bayanan da aka bamu gaskiya ne, cewar wannan harka ta kasuwa ce zalla shi ya sa muka zuba jarinmu. Kuma a matsayinmu na Eagles Hill muna farin cikin wannan jari namu a tsohuwar gwamnatin da ta shude, muna kuma kara farin ciki da rawar da za mu taka a wannan mai ci. Kuma an tabbatar mana cewar Najeriya za ta yi maraba da jari na waje a ko yaushe shi ya sa mu ka zo nan"

Abun jira a gani dai na zaman tabbatar da rikidewar birnin daga shiri na yan boko ya zuwa zahiri ta kasuwar da ba cuwa cuwa a cikinta.))