1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da Twitter

August 12, 2021

Najeriya ta cimma yarjejeniyar fara karbar haraji daga kamfanin sada zumunta na Twitter a shirin janye haramcin da aka yi wa kamfanin a makonnin baya.

https://p.dw.com/p/3yufV
Nigeria Katsina | Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

A wani abun da ke zaman alamun nasara a bangaren mahukuntan tarrayar Najeriya da suka dakatar da ayyuka na kamfanin sada zumunta na Twitter har na tsawon sama da watanni biyu.

Akalla sharruda guda zakwas ne, gwamnatin Najeriyar ta gindaya ga kamfanin da a baya gwamnatin ta zarge da kokarin tayar da tarzoma a kasar. Kuma daga dukkan alamu Twitter ta cika sama da biyar da suka hada da amincewa su biya haraji ko bayan bude ofishin a Najeriya, abun kuma da ya faranta ran gwamnatin da ke fadin ana dab da zuwa gaci na karshen rikicin.

Karin Bayani:  Rikicin Twitter a Najeriya ya dauki hankalin jaridun Jamus

Twitter CEO und Mitbegründer Jack Dorsey
Shugaban Kamfanin Twitter Jack DorseyHoto: AFP/P. Singh

Mahukuntan Najeriyar sun ce, a 'yan kwanakin da ke tafe, tana shirin sake kyale kamfanin ci gaba a cikin harkoki a kasar. A watan Yunin da ya shude ne, gwamnatin Najeriyar ta dakatar da kamfanin na Twitter da ta zarga da hadin baki da masu tayar da kayar baya da nufin yamutsa harkoki na gwamnatin kasar.

To sai dai kuma wani bayani na shugaban kasar bisa yakin basasa na kasar da kamfanin ya ce ya saba da ka'ida, inda har ya goge rubutun shugaban kasar, shi ne ya janyo tayar da jijiyar wuya a bangaren mahukuntan da suka zargi kamfanin da nuna fifiko ga 'yan aware na Biafra. Karin Bayani:  Takun saka tsakanin Twitter da gwamnatin Najeriya

Nigeria | Twittersperre: Mann benutzt Twitter in Lagos
Zargin amfani da Twitter a rikicin #EndSarsHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Ana kallon sulhun da idanun nasara a bangaren mahukuntan Najeriyar, da a baya suka sha sukar take hakki na 'yan kasar ko bayan mummuna ta'asar a bangaren kanana na masu kasuwar da ke raja'a ga kamfanin domin harkokinsu.

Duk da dubban miliyoyi na dalolin da suke samu a shekara, har ya zuwa yanzu, babu ko da kamfanin sada zumunta guda daya da ke biyan haraji a cikin tarrayar Najeriya. Wannan ya kawo karshen takaddamar da ta janyo tsaiko ga masu amfani da shafin a gudanar da hada-hadar kasuwanci a kasar mai yawan al'ummar da suka zarta miliyan dari biyu.