1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Fargaba game da gyaran kudin tsarin mulki

Uwais Abubakar Idris
January 26, 2018

Masu rajin kare demokradiyya a Najeriya sun nuna damuwa kan aikin gyaran kudin tsarin mulkin kasar inda suke cewar akwai yiwuwar abin ya lalace bayan da ya isa hannun jihohi ganin yadda aikin ke tafiyar hawainiya.

https://p.dw.com/p/2rb1P
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Sassa har goma sha biyar ne dai ake ta kokari na yi masu gyaran fuska a kundin tsarin mulkin Najeriyar a wannan yunkuri da ‘yan majalisar dokokin suka kaiga kammala nasu aikin inda ake jiran majalisun dokoki na jihohi su yi nasu dai ana fargabar abubuwan da ka iya faruwa yayin wannan aiki.

Muhimman batutuwa na baiwa kanana hukumomin ‘yancin gashin kansu da batun mika kasafin kudi kafin cikar shekara batutuwa ne da a baya jihohin suka dakile ganin yunkurin ganin sauya su. Shekaru 18 kenan ana irin wannan kokari ba tare da samun nasara ba, abinda ya sanya gamaiyyar kungiyoyin kare dimukurdiyya da suka kira kansu da abokan dimukurdiyya kokari na tabbatar da samun nasarar lamarin.

Nigeria Präsident Muhamadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugabannin majalisun dokokin kasarHoto: Novo Isioro

Abin da ke daga hankali a daukacin aikin na gyaran tsarin mulkin Najeriyar shi ne har zuwa wannan lokaci jihohi biyu ne na Benue da Cross River suka kaiga kammala amincewa da lamarin, yayin da sauran majalisun dokoki na jihohin Najeriyar ke jan kafa ka batu, lamarin da ya sanya ake ganin akwai yiwuwar sukurkucewa aiki kamar yadda Malam Sulaiman Garba Gora wanda ke cikin masu rajin ganin an samu yi wa tsarin mulkin Najeriyar gyaran fuska ya shaidawa wakilin DW a Abuja.

Yanzu haka dai ana cike da fatan samun gyara wadannan sassa na tsarin mulkin Najeriyar da mutane da yawa suka hakkake a karkace ya ke saboda a zamanin mulkin soja ne aka tsara shi. Aikin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska da a yanzu za a ce ya yi nisa kuma an fara jin kamshi kaiwa ga gaci to sai dai kamar a kan ce askin ya fi zafi in ya kai irin wannan mataki abin da ya sanya kungiyoyin rajin kare dimukurdiyya da suka kira kansu abokan dimukurdiyya bayyana damuwarsu har ma suka nemi a  maida hankali.