1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Alkalin alkalai zai gurfa a gaban kotu

Gazali Abdou Tasawa
January 12, 2019

A Najeriya kotun da'ar ma'aikata ta tuhumi alkalin alkalai na kasar Walter Samuel Nkanu Onnoghen kan kin bayyana hakikanin kadarorin da ya mallaka.

https://p.dw.com/p/3BSeo
Walter Samuel Nkanu Onnoghen Chief Justiz für Nigeria
Hoto: Ubale Musa

Kakakin kotun da'ar ma'aikatan Najeriya Ibraheem Al-Hassan wanda ya sanar da wannan mataki a wannan Asabar ya ce alkalin alkalan zai gurfana a ranar Litinin a gaban wasu alkalai guda uku a birnin Abuja. 

Sai dai bai bayar da cikakken bayani ba a game da takamaiman kadarorin da kotun da'ar ma'aikatan ke zargin alkalin alkalan da yin kwage kansu ba. Amma daga nata bangare fadar shugaban kasar ta Najeriya ta sanar da cewa kotun na zargin alkalin alkalan da boye wasu asusan ajiyar na banki da ke kunshe da makwadan kudade na Dalar Amirka da Euro da ma Pound. 

A karkashin dokokin Najeriya dai ya zamo dole ga manyan jami'an gwamnatin kasar kan su bayyana illahirin kadarorin da suka mallaka kana ba su da izinin mallakar wani asusu na ajiyar kudin kasashen waje. Tuni ma dai gwamnatin Najeriyar ta bukaci alkalin alkalan da ya ajiye aikinsa.