1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen yaki da cin hanci a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
October 17, 2019

A Najeriya shirin tonon silili da gwamnatin kasar ta bullo da shi wadanda cibiyar samar da bayanai a kan cin hanci da rashawa da tallafin gidauniyar MacArthur, na fuskantar kalubale.

https://p.dw.com/p/3RSBP
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Shekaru uku da fara aiwatar da wannan tsari na tona sili, inda gwamnatin ta sanya lada na kaso biyar cikin 100 da kuma kaso 2da rabi ga duk wanda ya tona asirin masu halin bera a kasar, a shekarar farko an samu 'yan Najeriya da dama da suka hura usur din ta hanyar tona asirin masu halin bera, abin da ya sanya gano makudan kudi na fitar hankali da aka sace. A kan wannan ne cibiyar Africmil ta gudanar da wani taro domin waiwaye adon tafiya a kan wannan shiri.

Gidauniyar MacArthur dai, ita ce ke samar da kudin gudanar da aikin tallafawa kungiyar don gudanar da ayyukanta har zuwa wannan lokaci na tsawon shekaru biyu. To sai dai rashin dokar kariya ga masu tonon sililin a Najeriya, na zama babbar matsala domin akwai mutane da yawa da a dalilin tona asirin sun rasa aikinsu wasu ma an jefa su gidan yari saboda kawai sun yi kokarin tona asirin masu halin beran, abin da Abdulazeez Abdulazeez manajan gudanarwa na kungiyar ya ce ya haifara da cikas sosai.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Bukatar majalisar dokokin Najeriya ta yi dokar kare masu tonon silili kan cin hanciHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Ko mai gwamnati ke yi a kan wannan batu? Mr Johnson Oludare mataimakin darakta ne a ma'aikatar kudi ta Najeriya kuma shugaban kwamitin kula da masu tonon sililin, ya ce:

"Tun daga lokacin da aka fara aiki da wannan tsari a watan Disamba na 2016, muna fuskantar kalubale saboda rashin dokoki kan tsarin aikin. Muna aiki domin shawo kan wannan matsala, majalisar dokokin da ta gabata ta yi aiki amma ba a cimma matsaya ba, yanzu mun tattaro wadannan dokoki kuma yanzu haka kwamiti na aiki don bai wa 'yan Najeriya dama su yi nazari. Ana ganin kamar ba a kare masu tonon silili ne saboda rashin wannan doka."

Mahalarta taron sun bayyana bukatar 'yan Najeriya su kara kaimi wajen neman lallai majalisar dokoki ta samar da dokar da za ta kare masu tonon sililin da kuma hukunta masu biris da umarnin mayar da wadanda aka kora a aikinsu, saboda sun tona asirin masu cin hanci da rashawa.