1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin ceto tattalin arziki

Ubale MusaSeptember 22, 2016

Bayan share tsawon lokaci ta na gwaji ta na sauyawa, gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar sauraro daga masana da nufin neman hanyar ceto tattalin arzikin kasar daga matsalar da ya shiga.

https://p.dw.com/p/1K3FE
Nigeria Flüchtlinge wegen der Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Kama daga shi kansa shugaban kasar ya zuwa ministoci na gwamnati dama manyan daraktoci na hukumomi na gwamnati dai sun share wunin yau suna daukar lacca ta kwarraru da nufin neman hanyar ceto tattalin arzikin kasar da ke halin ni 'yasu a yanzu. A karon farko a shekaru kusan 30 dai Najeriyar dai ta fuskanci matsin da babu kamarsa bayan da tattalin arzikin kasar ya yi kasa da kusan kaso biyu da digo daya a wattani ukun tsakiya na shekarar kacal.

To sai dai kuma gayyar masanan dai a fada ta Buharin na zaman damar hada hannu da nufin ceto kasar daga cikin ramar dake neman kada ita a yanzu.

"A lokacin da gwamnatin ke daukar zafi a aikinta na sake gyara tattalin arzikin kasar domin sauyi, ba za mu iya samun nasarar hakan ba mu kadai, muna bukata kuma muna neman taimakon 'yan kasuwa ciki dama wajen kasar, da kuma jihohi da kannanan hukumomi da majalisun tarraya da kuma bangaren shari'á da kuma ragowar 'yan kasar da ke sha'awa ta cigaba, muna da imanin cewar in mun aiki tare to kuwa za mu yi nasara"

Nigeria Reparatur von Handys
Hoto: picture-alliance / dpa

Alamun taren dai ta fara bayan da gwamnatin ta sauko daga dokin girma ta kuma saurari kwararru kama daga jami'o'i na kasar da kuma kamfanoni da ke zaman kansu da ma ragowar masana a bisa hanyar ceto tattalin arzikin da ke neman wucewa da sani na gwamnatin.

To sai dai koma wane irin agaji gwamnatin kasar take shirin bayarwa da nufin ceto ga kasuwar dai, mahukuntan da har ila yau kuma ke shirin wani kasafi ga kasar sun ce suna shirin kallon tsaf da nufin sanin makama ta kasar a badin a fadar karamar ministar kasafin kudin kasar zainba Shamsuna Ahmed.

To sai dai kuma ko ma ta ina masu mulkin na Abuja ke shirin bi da nufin fitar da wando ta tsakar ka dai, ya zuwa yanzu gwamnatin ta Abuja tana ji a jiki sakamakon masassarar da ke zaman mai zafi da kuma ta tada muhawara cikin kasar game da gazawa ta gwamnatin.

Karikatur Nigeria Wirtschaft Rezession
Hoto: DW

Tuni dai jamíyyar PDP ta adawa ta kalubalanci Buharin da maida kasar in da ya same ta a bara ko kuma ya sauka bisa kujera ta shugabanci na kasar da tace ya kasa. Shawarar kuma da Abujar ta ce ba ta da zarafi daga bakunan 'yan lemar da suka tafka ta'annati kuma ke neman wuce makadi da rawa a fadar lai Mohammed da ke zaman ministan labarai na kasar.

"Suna fada mana mu daina maganar baya, amma kuma har yanzu bayan ce ke ta dago kanta, ka gani a shekara ta 2008 Najeriya na da kudin ajiya na wajen da ya kai Dalar Amurka miliyan dubu 62, amma ya zuwa shekara ta 2015 ya koma dala dubu 30. A shekara ta 2007 rarar ajiyarmu ta kai Dala miliyan dubu tara amma ya zuwa shekara ta 2015 ta koma Dala miliyan dubu biyu. A wannan lokaci da muke magana Indunusiya ta daga nata kudin ajiyar daga Dala biliyan 60 a shekara ta 2008 ya zuwa biliyan 120 ya zuwa bana. Bayan haka kuma shekrun PDP sun kai ga ninka yawan bashinmu da ke waje da kaso 200. saboda haka ba shi fitowa daga bakin PDP su bukaci shugaban kasa ya ajiye aikinsa saboda batu na tattali na arziki"

Abun jira a gani dai na zaman tasiri na sabuwa ta dabara ta Abujar ga kasar da hakurin al'umma ke kara ragewa ga matsin da suke ji sakamakon laifin da ba shi ubangida cikin kasar