1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan zargin yunkurin juyin mulki

Uwais Abubakar Idris LMJ
May 5, 2021

Jamiyyar adawa ta PDP da kungiyoyin shiyya a Najeriya, sun bayyana zargin da gwamnatin kasar ta yi na cewa ta gano makarkashiyar yi mata juyin mulki da kokarin kawar da hankalin al'umma daga matsalolin da kasar ke ciki.

https://p.dw.com/p/3t0cH
Nigeria Präsident Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya Hoto: Reuters/L. Gnago

Kasa da sa'o'i 24 da mahukuntan Najeriyar suka fitar da wannan zargi na cewa, sun bankado yunkurin kifar da gwamnatin tana  kumfar bakin za ta ladabtar da wadanda ke da hannu a wannan yunkuri da  rundunar sojojin Najeriya ta fara fito da shi a fili ne dai, aka fara mayar da martani a kai tare ma da nuna tababa ga daukacin al'amarin. 

Karin Bayani: Barazarar tsaro ga zabukan 2023 a Najeriya

Jam'iyyar adawa ta PDP da ma kungiyoyin shiyoyin kasar na Afenifere ta 'yan kabilar Yarabawa da ta Dattawan Arewa a Najeriyar dai, sun kasance kan gaba wajen mayar da martanin. 

Karikatur Cartoon Nigeria
Ba a jima da canja manyan hafsoshin soja a Najeriya ba, amma ba ta sauya zani baHoto: Abdulkareem Baba Aminu/DW

Sun yi zargin cewa gano yunkurin juyin mulki ba da fatar baka ake yinsa ba, domin inda ba kasa ake gardama kokuwa. Ta dai kai ga shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari fitowa fili ya na mai cewa shiru-shiru fa ba tsoro ba ne, to sai dai tuni wasu 'yan Najeriya irin su Alhaji Musa Ardo da ke fafutukar wanzar da zaman lafiya ke bayyana cewa, fatansu dai kasa ta zauna lafiya. A yayin da wannan ke faruwa ga mafi yawan al'ummar kasar ba su nuna ko gezau ba, domin abin da ya fi damunsu a yanzu shi ne matakai da gwamnatin ta ce tana dauka na shawo kan matsalar tsaro da tafi addabar rayuwarsu da jefa su cikin mawuyacin hali.