1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matasa masu dinka kwallo a Gombe

Amin Sulaiman Mohammed/ SBAugust 24, 2016

Yanzu haka wasu kungiyoyin kwallon kafa na sayen kwallon ne da kuma takalman bugawa a wurin wadan nan Guragu masu sana'ar dinka kayan wasan na kwallon kafa.

https://p.dw.com/p/1JoBo
Afrika Soweto Stadtansichten Riesiger Fussball an Einkaufszentrum
Hoto: picture-alliance/Bildagentur-online


A baya dai ana daukan cewa sai babbar masana’anta da ke kasashen ketare ne ke iya yin kwallon da ake wasannin kwallon kafa da shi, da kuma takalma da ake buga kwallon saboda wuyar sarrafawa da kuma karancin kayayyaki da ma kasuwarsu musamman ganin yadda ‘yan Najeriya suka rena kayan da ake yi a cikin gida. Yayin da ake zaton wuta a makera sai kuma ga ta a masaka don kuwa wasu matasa ne masu nakasa da Allah ya horewa basirar dinka kwallayen kafa da takalma suna sayarwa domin dogaro da kan su.

A kowane mako wadan nan bayin Allah za su iya yin kwallaye fiye da 50 da takalma sama da wari 50 matukar akwai masu saye. Masu amfani da kwallayen da takalman da suka sarrafa sun ce suna da kwari kuma sun fi jure wuya sabanin wadan ake shigo da su da ke da tsada kuma cikin kankanin lokaci suke lalacewa.

Wadan nan bayin Allah wanda wa da kani ne, su na kuma koyar wa matasa nakasassu da masu lafiya wannan sana’a wacce suka ce idan da hukumomi da kungiyoyi na sayen abinda suke sarrafawa da sun fadada ayyukan na su. Masharhanta dai kamar Lawan Ibrahim Pantami na ta madina na ganin indan da gwamnati za ta tallafawa wadan bayin Allah, to da an rage barace-barace da ma rage zaman banza tsakanin matasa.

Nigeria Frauenfußball FC Robo
Hoto: DW/S. Olukoya