Najeriya: Matashi mai sana'ar fawa a Kaduna

Kabiru Sani wani matashi ne mai shaidar karatun gaba da sakandare a jihar Kadun dake Najeriya ya rungumi sana'ar fawa domin dogaro da kai

Matashin mai shekaru 31 a yanzu yana cikin mahautan da ake alfahari da su a mahautar unguwar sabon tasha da ke garin Kaduna. Kawo yanzu ya samar wa kansa aikin yi ba tare da ya dogara da wani ba.

Sana’ar fawa dai kamar sana’o’i irinsu noma na cikin sana’o’in kasar Hausa da wasu matasa ‘yan boko kan kaurace musu koda kuwa sun taso sun ga ana irin wadannan sana’o’i a gidajensu. To amma Kabiru Sani bai shiga cikin jerin irin wadannan matasa ba.

Duk da jinjina da ake wa matashi Kabiru Sani, a yanzu ya ce hauhawar farashin dabbobi a kasuwanni na cikin kalubalen da suke kawo masa cikas.

Bayanai masu kama

Himma dai Matasa | 10.04.2019

Kade-kade da waka don dogaro da kai

Himma dai Matasa | 13.03.2019

Sana'ar gyaran gashi a Abuja

Himma dai Matasa | 21.03.2019

Mai kera tukwanen gargajiya a Kaduna