1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matashi mai sana’ar kiwon kifi.

December 12, 2018

A jihar katsina da ke Najeriya wani matashi da ya kammala karatun Diploma tsawon shekaru babu aikin yi ya kama sana'ar kiwon kifi.

https://p.dw.com/p/39wSu
Mittelmeer Fischfang
Hoto: imago/G. Leber

Matashin yace sakamakon sana'ar kiwon kifin da ya dukufa ya samu dukiya mai tarin yawa wanda hakan ya cire masa shaa'awar aikin gwamnati kuma ya koyawa wasu matasa sana'ar su ma suna dogaro da kansu.

Matashin, Haladu Abdullahi Ajiwa yace sa rai a aikin gwamnatin tamkar zaman jiran gawon shanu ne ganin ya dauki tsawon shekaru da kammala karatunsa yana ta fafutuka amma babu aikin, wannan yasa ya yankewa kansa shawarar neman mafita.

Kenia USA Fotoreportage von Kogelo Dorf von Obamas Vorfahren
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Abun da ya ja hankalina shine na gama karatun sakandire na kuma yi diploma amma babu aikin yi ganin da na yi ta yawo ma'aikatu ko kamfanoni ina neman aiki shine na yanke shawarar na koyi wani abu wanda zan dogara da kaina ba sai na kalli gwamnati ko wani ya taimaka mun ba. Na je wajen wadanda suka iya sana'ar suka koya mun na iya, nima na kama yi kusan shekaru uku kenan muna yi babu abunda muke gani sai riba.

Zama ga matashi babu aikin yi ya kan sanya shi cikin yanayi mawuyaci. Haladu Abdullahi Ajiwa yace ya fuskanci kalubale yayin sana’ar.

A gaskiya an sha wahala saboda akan wuni ba'a ci ba kuma ga nauyin iyaye amma cikin ikon Allah sana’ar ta kankama.