1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar man fetur ya addabi 'yan Najeriya

January 4, 2018

Matsalar man ferur a Najeriya na nema ya gagari kundila, yayin da dillan man ke dora laifi akan kamfanin mai na kasa NNPC, a nasa bangaren kamfanin na zargin 'yan kasuwar da neman kara farashi.

https://p.dw.com/p/2qMPK
Nigeria Lagos Benzinpreis
Hoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Duk da cewa yanzu kamfanin man kasar na NNPC ya yi nasarar kai karshen matsalar a Legas da ke zama cibiya ta kasuwanci da Abuja babban birnin kasar ga dukkan alamu har yanzu da sauran aiki game da makomar harkar man fetur da al'ummar kasar ke dogaro a kai. Tashin farashin gangar danyen man ta sanya ba riba a tunanin manyan dillalan man da ke cewar suna tafka asara mai yawa wajen shigo da man daga waje sannan su sayar a kan farashin Naira 145 kan kowace lita.