1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matsalolin aikin jin kai a arewa maso gabas

November 28, 2019

Shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ya fada cikin mawuyacin hali na matsalolin jin kai da kuma tabarbarewar tsaro saboda sabbin hare-hare da mayakan Boko haram ke kaiwa a sassan jihohin Borno da Yobe.

https://p.dw.com/p/3TuKD
Symbolbild Nigeria Bama Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

Ko a laraba mayakan Boko Haram sun tarwatsa garin babban gida da ke karamar hukumar Tarmuwa tazarar kilomita 50 daga Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe.

Dubban ‘yan gudun hijira na kwarara Maiduguri da sauran yankuna domin tsira daga hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai musu kan fadan da ake gwabzawa tsakanin Sojojin Najeriya da yan Boko Haram a wasu yankunan jihar Borno da wasu yankuna na jihar Yobe.

Wannan yanayi ya haifar da kalubalen tsaro da matsaloli ga ayyukan jin kai saboda yadda daruruwan mutane ke kwashe kwanaki su na tafiya a kafa domin zuwa wuraren da ke tsaro don samun abin da za su ci.

Nigeria Ausgabe von Nahrungsmitteln durch Hilfsorganisation
Agajin abinci ga 'yan gudun hijira a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Mata da kanan yara su ne suka fi fama da matsalolin rashin wurin kwana da kuma abinci inda yara da dama suka fara kamuwa da cutattuka musamman saboda sanyi da rashin matsuguni.

Kungiyoyin da ke gunadar da ayyukan jin kai a yankin sun danganta tururuwar da jama’a ke yi zuwa Maiduguri da sauran wurare da rashin tsaro gami da karancin kulawa.

Masana tsaro dai na ganin babbar matsalar da ake samu na rashin fahimtar juna tsakanin gwamnatocin jihohin da ke fama da kalubalen tsaro da kuma jami’an tsaro shi ne ya haifar da koma bayan da ake samu a harkokin tsaro a bakin gabar tafkin Chadi.