1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na fushi kan wulakanta 'ya'yanta a Kamaru

July 13, 2017

Tarrayar Najeriya da kamaru sun sake fadawa cikin dambarwar dipolomasiya sakamakon ikirarin cin zarafin 'yan Najeriya a yankin Bakassi tare da wulakanta 'yan gudun hijira da Boko Haram ta raba da matsugunansu.

https://p.dw.com/p/2gT2b
Kamerun Präsidenten Paul Biya & Muhammadu Buhari Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

A cikin farkon wannan mako ne wani rikicin biyan harajin kwale-kwale ya yi sanadiyar kisa na 'yan Najeriya kusan 100 a yankin Bakassi da Jamhuriyar kamaru ke iko a kansa a yanzu. Ana zargin jami'an tsaron Kamarun da kai hari a kan mazaunan na Bakasi da ake zargi da kin biyan harajin a wani abun da ke zaman na baya-baya nan cikin takkadama tsakanin al'ummar yankin.

Nigerianischer Soldat auf der Halbinsel Bakassi
Sojojin Kamaru ake zargi da cin zarafin 'yan Najeriya a BakassiHoto: AP

Harin ya harzuka mahukuntan tarrayar Najeriyar da ke masa kallon karya yarjejeniyar unguwar Green Tree ta kasar Amirka da ta tanaji zama a cikin 'yanci a bangaren al'ummar tarrayar Najeriyar da ke yankin da kotun duniya ta mika wa Kamaru.

Tuni fadar mulki ta Abuja ta mika sammaci ga jakadan kamaru da ke tarrayar Najeriyar, sannan kuma tana shirin tura ministocinta  biyu zuwa Yaoundé da nufin nunin bacin ranta, a cewar  ministan cikin gidan tarrayar Najeriyar Abdurahman Bello Dambazau.

Sai dai  bacin ran tarrayar najeriyar bai tsaya a kan cin zarafin 'ya'yanta da ke a Bakassin ba, tuni ma dai ya tsallaka zuwa ga 'yan gudun hijirar Boko Haram da kamarun ke tilasta wa dawowa gida cikin halin kunci. Abun da Abujar ke kallon ba daidai ne ba, sannan kuma ya saba wa ka'idar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Flüchtlingslager Minawao in Kamerun
Hoto: DW/M.-E. Kindzeka

Akalla 'yan Najeriya 2,600 ne kamarun ta tilasta wa dawowa cikin gida. Ko a karshen wata Yuni an tasa keyar wasu 'yan gudun hijirar 887 ya zuwa garin Banki da ke kan iyaka ta kasashen guda biyu. Abin kuma da har ila yau ministan cikin gidan tarrayar Najeriyar ke kallon cewa an saba .

Ana kallon kasancewar Paul Biya a Abuja da kuma ziyara shugaba Muhammadu Buhari zuwa birnin Yaoundé sun taka muhimmiyar rawa wajen sauyin yakin da a baya ya nemi gagarar kundila tsakanin kasashen biyu. Da tsoma bakin manyan kasashen duniya irin nasu Amirka da Faransa ne aka kai ga sulhunta tsakanin makwabtan kasashen Najeriya da kamaru.