1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na hana walwalar addini inji Amirka

Binta Aliyu Zurmi
December 8, 2020

A karon farko Amirka ta saka Najeriya a jerin kasashen da ke hana walwala ta addini. Wannan na zuwa ne yayin da alummar kasar mabiya addinin Kirista ke nuna damuwarsu game da karuwar matsalar tsaro a kasar.

https://p.dw.com/p/3mNpk
US-Außenminister Pompeo in Israel
Hoto: Patrick Semansky/Pool/picture alliance

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ne ya ambata Najeriyar a matsayin kasar da ke tattare da matsaloli a bangaren addini. Mr. Pompeo ya kara da cewar wannan batu na nufin idan har aka yi wa addini hawan kawara to za su maida martani.

Sauran kasashen da Amirka ke kuka da su, sun hada da Saudi Arabiya da Pakistan Iran da China. Amirkan dai ba ta fayyace dalilan da su ka sa ta saka Najeriya a cikin wannan jeri na kasashe ba, amma dai a rahotonta da ta ke gabatarwa na shekarar-shekara ta duba koke-koken al'umma musamman ma na mabiya tafarkin Shi'a a kasar.