1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na nazarin dokar kariya ga masu bada bayanan sirri

February 4, 2013

Majalisar wakilan kasar ta gudanar da taron muhawarar jin ra'ayin jama'a a game da kafa dokar da zata bada kariya ga masu bada bayanai na aiyyukan da suka sabawa doka a kasar.

https://p.dw.com/p/17Xy8
Hoto: picture-alliance/dpa

A wani mataki da ka iya yin tasirin wajen yaki da aikta miyagun laifuffuka musamman na ta'adanci da cin hanci da rashawa a Najeriyar, majalisar wakilan kasar ta gudanar da taron muhawarar jin ra'ayin jama'a a game da kafa dokar da zata bada kariya ga masu bada bayanai na aiyyukan da suka sabawa doka a kasar.

Samar da doka da zata bada kariya ga mutanen da suka bada bayanai bisa radin kansu na aiyyukan assha da suka hango ana aikatawa a kowane sashi na Najeriya na zama matakin baya- bayan nan da ake yi domin shawo kan masu aikata miyagun laifuffuka musamman na ta'adanci da ma cin hanci da rashawa da sauran laifuffukan da ke zama barazana ga zaman lafiya da ci gaban kasar.

Rashin samar da kariya ga masu niyyar bayar da bayanai na aiyyukan assha a asirce ga hukumomin tsaron Najeriyar shi ya sauya halin da ada can aka san yan kasar das hi, domin su hanzarta daukan matakai na dakile masu aikata laifi da aka dangata shi da dalilin da ke sanya yan Najeriyar da dama dari-dari da tunkarar jami'an tsaro domin basu bayani da zasu iya taimakawa a wannan fannin, shine ya sanya kama aikin kafa dokar. To ko me yan majalisar ke hange zai iya zama tasirin wannan sabon mataki ga yaki da ta'addanci a Najeriyar? Hon Hassan Albadawi na cikin yan majalisar da suka tattauna a kan wannan batu.

‘'Zai taimaka kwarai da gaske a cikin sha'anin tsaro da muke ciki, domin muddin dai mutum ya tabbata ba zai cutu ba in ya fadi wani bayani, kuma jama'a zasu amfana da shi, shi kuma zai amfana dashi to kuwa zai taimaka. Kaga mutane ai suna kin zuwa ne su bada shaida ko bayanai ga jami'ai domin gudun wulakanci, don idan jami'an tsaro suka zo sai su ce ai kaine ma mai laifin. Don kare irin wadannan al'ammura aka bukaci cewa a duba irin wadannan dokoki, kuma a baiwa mutane karfin guiwar abinda suka samu . Wannan zai baiwa mutane karfin guiwar taimakawa a wajen sha'anin tsaro da ya zamo mana wani gagarumin wahala''.

Anschlag auf ein UN Büro in Abuja Nigeria
Harin ta'addanci a ofisoshin Majalisar Dinkin Duniya a AbujaHoto: dapd

Samun nasarar yaki da ta'adanci da ma sauran miyagun laifuffuka dai aiki ne da kwararru ke danganta samar cikakkiyar nasararsa a kan samun bayanai a asirce daga yan kasa, ta yadda kowane mutum ka iya zama dan sanda mai sanya idannu wajen samar da bayanai. To sai dai ba haka lamarin yake a Najeriya ba.

Wannan na da alaka ne da irin bita-da- kulli da akan yiwa wanda ya bada shaida ga jami'an tsaro a Najeriya, abinda a lokuta da dama kan sanya yan kasa da kau da kai ba kawai ga masu aikata laifin ba, har ma da duk wani bayani da ka iya taimakawa a baya. Abinda ya sanya tambayar wane tabbaci za'a samu cewa lallai tsarin zai samar da kariya, har ma da bada tukuici ga masu bada bayanan sirri don kare aikata miyagun laifuffuka a kasar? Hon Ahmed Ali wanda shine shugaban kwamitin kula da harkokin shari'a na majalisar wakilan Najeriya da ya jagoranci zamn kwamitin a kan wannan batu.

‘'Wanan abu ne mai sauki idan kaje ka samu bayani, misali ka baiwa ministan shari'a koma wani shaihi ne a unguwarku ka bashi, idan shaihin nan yaje ya bada sunanka, to za'a tuhume shi, kaga akwai irin wadannan abubuwan da aka sanya a cikin doka, domin in ma daga baya aka sani, abinda yan Najeriya suka ce shine a sanya a cikin dokar , don haka dokar tana da tasiri sosai''.

Aikin yaki da aikata miyagun laifuffuka kama daga na ta'adanci zuwa ga cin hanci da rashawa da ma sauran aiyuka na tir na zama lamari da ake gaza ganin tasirinsa duk kuwa da zarattan jami'an tsaron da Najeriyar ke da su da ake kasaftawa bilyoyin Naira domin yakar matsalar.

Bombenanschlag Nigeria
Alamar rashin tsaro a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

Duk da cewa hukumomin yaki da aikata miyagun laifuffuka da ma kungiyoyin masu zaman kansu da kan tallafa sun nuna amanna da wannan kuduri, amma abin jira a gani shine ko wannan dubara ta bullo da dokar da zata samar da kariya ga masu bada bayanan sirri ga jami'an tsaro na iya sauya batun, musamman sanya batun asirta mai bada bayani da ma bashi tukuici a kan hakan.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris

Edita: Umaru Aliyu