1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

International Crisis Group ta binciki rikici a Najeriya

Salissou Boukari
July 26, 2018

Wani rahoto da cibiyar bincike ta kungiyar sasanta rikici na kasa da kasa ta fitar a wannan Alhamis, ya ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a Najeriya, ya rubanya na Boko Haram.

https://p.dw.com/p/3264U
Nigeria Angriff von Nomaden im Bundesstaat Plateau | Sicherheitskräfte
Hoto: Reuters/Reuters TV

Kungiyar ta ce yawan mutanen da suka mutu a rikicin manoma da makiyaya ya rubanya har sau shida adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Boko Haram tun daga farkon wannan shekara kawo yanzu.

Cibiyar ta International Crisis Group, ta sanar cewa kokarin da ake yi na samun filayen noma ko na kiwo shi ke kara rura wutar rikicin sakamakon yawaitar al'umma a kasar da take da mafi yawan al'umma a Afirka, wanda hakan ke haifar da babbar barazana ta tsaro ga Najeriya.

rahoton ya ce akalla mutane 1,500 ne aka kashe sakamakon rikicin da ake dangantawa na tsakanin manoma da makiyaya tun daga watan Satumba na 2017, wanda cikin wannan adadi fiye da mutane 1,300 sun mutu ne a tsakanin watan Janairu zuwa watan Yuni na wannan shekara.