1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikici ya mamaye zaben Kano

Ahmed Salisu
March 23, 2019

Al'ummar jihar Kano sun koka game da abinda suka kira amfani da 'yan bangar siyasa wajen tada hankali da hana jama'a gudanar da zaben gwamna da aka karasa a wannan Asabar.

https://p.dw.com/p/3FZAD
Symbolbild Gewalt in Nigeria
Hoto: SEYLLOU DIALLO/AFP/Getty Images

Ana dai gudanar da zaben na yau ne a wasu mazabu a kananan hukumomi 28 daga cikin 44 da ake da su a jihar kuma hankali ya fi karkata ga mazabar nan ta Gama da ke karamar hukumar Nasarawa a cikin kwaryar Kano din, inda aka bayyana cewar 'yan bangar siyasa sun shiga mazabar kana sun kori masu kada kuri'a a rumfunan zabe daban-daban.

Haka ma abin ya ke a kananan hukumomin Rimin Gado da Doguwa da Kibiya inda nan aka bada labarin samun tashin hankali da lalata kayan zabe da kuma cin zarafin masu kada kuri'a da su kansu malaman zaben.

A wasu yankunan kuma rahotanni na nuna cewa ana amfani da kudi wajen jan hankalin masu kada kuri'a. Tuni dai jam'iyyar PDP da ke adawa a jihar ta ce ba ta amince da zaben ba har ma shugabanta Rabi'u Suleiman Bichi ya bukaci a soke zabe saboda ya sabawa dokokin zabe da ake amfani da su a Najeriya din.