1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabon sumame kan Boko Haram

Salissou Boukari
January 9, 2018

Sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar sojojin kasashe makwabta sun ayyana wani babban sumame kan mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2qamA
Symbolbild Nigeria Luftwaffe
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Sojoji na kasashen Kamaru Chadi Nijar da kuma Najeriya sun shirya wannan sumamen ne a wani mataki na zakulo shugabannin kungiyar Boko Haram musamman ma Abubakar Shekau da suke samun malaba a cikin dajin Sambisa, da kuma Almansur Nur da ke yankin tafkin Chadi. A cewar rundunar sojojin ta Najeriya, tuni dai suka halaka daruruwan mayakan yayin da wasu da daman gaske suka mika kansu a cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan.

A cewar wani babban jami'in soja da ke Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya, tuni sojojinsu suka raunata Mamman Nur tare da halaka daya daga cikin matansa yayin wasu hare-hare ta sama da suka kai a maboyarsa, yayin da shi kuma Abubakar Shekau ke a matsayin tamkar dokin da ya gaji wanda batun kamashi batu ne na dan lokaci a cewarsa. Mai magana da yawun rundunar sojojin ta Najeriya Sani Usman Kuka Sheka ya ce sumamen ya haifar da samun nasara mai tarin yawa kan mayakan.