1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sankarau ta kashe mutane 1,000

Yusuf Bala Nayaya
May 12, 2017

Wannan annoba ta cutar sankarau dai ta zamo mafi muni cikin shekaru tara da suka gabata a Najeriyar da ke a Yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/2ct5W
Nigeria Falumata Muhammed trotzt Boko Haram
Hoto: DW/A. Kriesch

Sama da mutane 1,000 ne suka rasu sakamakon cutar sankarau a Najeriya dadin da ke zama na mutane 1,069 tun daga karshen shekarar 2016 kawowa yanzu, kamar yadda cibiyar yaki da bazuwar cututtuka a Najeriya ta bayyana a ranar Jumma'a.

Wannan annoba dai ta zamo mafi muni cikin shekaru tara da suka gabata a Najeriyar da ke a Yammacin Afirka. Akwai mutane 13,420 da ake zargin sun harbu da kwayoyin cutar kamar yadda rahotanni suka nunar bayan nazari a jihohin da ke Arewa maso Yammacin Najeriya inda lamarin yafi kamari.

Ana dai fargaba ta samun karanci na allurar ta sankarau mai lakabin C a duniya , abin da ya sanya Najeriya ke fuskantar sanya a fafutukar kawar da cutar mai saurin kisa.